Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ƴan bindiga sun raunata mutane da dama a Isra'ila
Aƙalla mutum bakwai ne suka samu raunuka bayan wasu mutane ɗauke da bindiga suka buɗe wuta a wurare daban-daban a Birnin Kudus, kamar yadda hukumomin Isra'ila suka shaida.
Maharan sun buɗe wuta kan wata mota ƙirar bas a wani wurin ajiye motoci kusa da bangon birnin mai ɗumbin tarihi.
Yanzu haka dai ƴan sanda sun shiga neman waɗannan mahara waɗanda suka tsere bayan harin da suka kai.
Wani mai magana da yawun ƴan sanda ya shaida wa kafofin watsa labarai cewa a hukumance an ɗauki wannan harin a matsayin hari na ta'addanci. Ɓangaren bayar da agajin gaggawa na ƙasar ya ce yanzu haka yana kula da mutane da dama da suka raunata.
Babu tabbaci kan takamaimai adadin ƴan bindigar da suka buɗe wutar, sai dai wata kafar yaɗa labarai ta ƙasar ta ruwaito cewa akwai aƙalla mutum biyu da ake zargi da ƴan sanda ke nema.
Wani bidiyo da aka wallafa a shafin sada zumunta ya nuna yadda ƴan sanda da ke cikin shiri ɗauke da makamai suka hallara a wurin da lamarin ya faru. Kafar watsa labarai ta Times of Israel ta ruwaito cewa akwai aƙalla mutum guda cikin waɗanda suka kai harin da sai da ya jira bas ɗin ta isa tasharta sa'annan ya buɗe wuta kan fasinjojin ciki.