Real za ta buga Copa del Rey ba tare da Mbappe da Bellingham ba

Asalin hoton, Getty Images
Real Madrid za ta buga Copa del Rey ba tare da Kylian Mbappe da Jude Bellingham, in ji koci Carlo Ancelotti.
Ranar Laraba Laganes za ta karɓi bakuncin Real Madrid a Copa del Rey zagayen kwata fainals.
Mbappe da Bellingham za su bi sawun masu jinya a ƙungiyar da suka haɗa da Eduardo Camavinga da David Alaba da Antonio Rudiger da kuma Eder Militao da Dani Carvajal da suka daɗe suna jinya.
Mbappe ƙyaftin ɗin tawagar Faransa, mai shekara 26 ya ci ƙwallo 21 a wasa 33 tun bayan da ya koma Santiago Bernabeu kan fara kakar nan daga Paris St Germain.
Shi kuwa Bellingham ɗan ƙwallon tawagar Ingila, mai shekara 21 ya zura ƙwallo 10 a wasa 30 a ƙungiyar ta Sifaniya.
Madrid, wadda take ta ɗaya a kan teburin La Liga da maki 49 bayan wasa 22 tana da tazarar maki ɗaya tsakaninta da Atletico Madrid ta biyu, Barcelona ce ta uku.
Real Madrid za ta yi wasanni masu zafi nan gaba a lokacin da ƙungiyar ke fama da ƴan wasa da yawa da ke jinya.
Bayan wasan da Real Madrid za ta yi a gidan Leaganes ranar Laraba daga nan za ta kece raini da Manchester City gida da waje a Champions League a wasan cike gurbi.
Real Madrid ba ta ɗauki ɗan wasa ba a Janairun nan, yayin da Manchester City ta sayi ƴan wasa biyar, ciki har da Nico da kuma Omar Marmoush.









