Ɓoyayyar taswirar da ka iya samar da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya

Tsohon Firaministan Isra'ila Ehud Omert riƙe da taswirar da ya tsara da ke nuna ƙasar Israi'la da ƙasar Falasɗinawa, a cikin maslahar ƙasa biyu
Bayanan hoto, Tsohon Firaministan Isra'ila Ehud Omert ya bayyana maslahar ƙasa biyu a 2008
    • Marubuci, Paul Adams
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Diplomatic correspondent
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 5

''Nan da shekara 50 mai zuwa, ba za ka samu shugaban Isra'ila ɗaya da zai kawo irin wannan tsarin da na kawo maka a yanzu ba.''

"Ka sa hannu! ka sa hannu mu kafa tarihi!''

A shekarar 2008 ke nan. Firaminista Ehud Olmert na roƙon shugaban yankin Falasɗinawa ya amince da yarjejeniyar da yake ganin za ta kawo zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya.

Maslaha ce ta samar da ƙasa biyu - wani abu da zai yi wahala a yanzu.

Da ace an aiwatar da shi, da an samar da ƙasar Falasɗinawa a kan fiye da kashi 94 cikin 100 na Gaɓar Yamma da aka mamaye.

Taswirar da Olmert ya zana a yanzu haka ta zama wani abu da kamar wuya ya faru.

Mutane da dama sun fassara ta a shekarun da suka gabata, amma ba a taɓa nuna wa kafafen yaɗa labarai ba.

Sai yanzu.

Taswirar Ehud Omert da ke nuna ƙasar Israila da na Falasɗinu a gefe da gefe
Bayanan hoto, Taswirar Ehud Olmert ta maslahar samar da ƙasa biyu, da ke nuna ƙasar Isra'ila da na Falasɗinawa a gefe da gefe
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A cikin gajeren shiri mai suna ''Israel and the Palestinians: The Road to 7th October'' wadda mai shirya finafinai Norma Percy ta shirya, wanda za a fara samun shi a iPlayer daga ranar Litinin, Olmert ya bayyana taswirar da ya ce ya nuna wa Mahmoud Abbas a wani taro a birnin Qudus ranar 16 ga watan Satumban 2008.

''Wannan ne karo na farko da na bayyana wa kafafen yaɗa labarai wannan taswirar,'' kamar yadda ya shaida wa masu shirya fim ɗin.

Taswirar ta fayyace yankin da Olmert ya bayar da shawarar Israi'la ta karɓe, wato kashi 4.9 cikin 100 na Gaɓar Yamma.

Yin hakan zai haɗa da manyan matsugunan Yahudawa - kamar yadda wasu tsare tsaren da aka yi a baya tun daga shekarun 1990 ke nunawa.

A nata ɓangaren, Firaministan ya ce ita ma Isra'ila za ta hakura da iyakar wannan girman yankin nata, ta ɓangaren yankin Gaɓar Yamma da kuma Zirin Gaza.

Yankunan Falasɗinawan biyu za su haɗu ta hanyar ƙarƙashin ƙasa ko babbar hanya, kuma, wannan ma abu ne da aka tattauna tun a baya.

A cikin gajeren fim ɗin, Olmert ya tuna da amsar da shugaban yankin Falasɗinawa ya ba shi.

''Ya ce: Firaiminista, wannan abu ne mai muhimmanci. Abu ne mai muhimmanci sosai.'

Tsarin Olmert ya haɗa da shawarar yadda za a samu maslaha kan batun birnin Qudus mai cike da sarƙaƙiya.

Kowane ɓangare za su iya samun iko da wasu ɓangare na birnin a matsayin babban birninsu, yayin da gudanarwar birnin da wuraren ibada da yankunan da ke kusa da su, za a miƙa su hannun kwamitin amintattu da ya haɗa da Isra'ila, yankin Falasɗinawa, Saudiyya, Jordan da kuma Amurka.

Tasirin da aiwatar da taswirar zai yi ga matsugunan Yahudawa a lokacin, da zai kasance mai girma.

Da ace an aiwatar da shirin, gwamman garuruwa da ke warwatse a Gaɓar Yamma da kuma yankin Jordan Valley, duk da an kwashe su.

A lokacin da tsohon Firaministan Isra'ila Ariel Sharon ya tilasta wa dubban Yahudawa da ke zaune a Zirin Gaza a 2005 ficewa daga yankin, masu sassaucin ra'ayi a Isra'ila sun yi wa hakan kallon babban abin damuwa ga ƙasar.

Kwashe akasarin mutanen da ke Gaɓar Yamman zai iya kasancewa matsalar da ta fi wancan girma, wanda ya haɗa da dubban mazauna, kuma hakan na da barazanar zama rikici.

Sai dai ba a kai ga hakan ba.

A ƙarshen tattaunawar tasu, Olmert ya ƙi amincewa ya miƙawa Mahmoud Abbas kwafin taswirar sai dai in ya amince ya sanya hannu.

Abbas ya ƙi amincewa, a cewar sa, ya na buƙatar ya nuna wa ƙwararru a ɓangarensa taswirar domin tabbatar da cewa sun fahimci ainihin abin da aka gabatar musu.

Olmert ya ce su biyun sun amince ayi taron ƙwararru a fannin taswira a rana ta gaba.

'' Mun rabu a ranar, kun gane, kamar mu na da shirin ɗaukar wani babban mataki na tarihi,'' in ji Olmert.

Ba a gudanar da wannan taron ba.

A lokacin da su ke hanyar komawa a motarsu daga birnin Qudus a wannan daren, shugaban ma'aikata na fadar shugaba Abbas, Rafiq Husseini, ya tuno yanayin da suke a cikin motar.

''Babu shakka mun sha dariya,'' in ji shi a cikin fim ɗin.

Falaɗinawan sun yarda cewa shirin ba mai yiwuwa bane.

Olmert da ke tsumu-tsumu cikin badaƙalar cin hanci, ya riga ya sanar da shirinsa na ajiye aiki.

''Abin takaici ne cewa Olmert, duk da kirkinsa ... mutum ne dai bai yi nasara ba.,'' in ji Husseini, '' don haka, ba inda za muje da wannan shirin nasa.''

Yanayin da Gaza ke ciki a lokacin ya sake tsananta alamura.

Bayan shafe watanni ana kai harin rokoki daga yankin da Hamas ke da iko, Olmert ya bayar da umurnin kai gagarumin farmaki mai suna ''Operation Cast Lead'' a ƙarshen watan Disamba, wanda ya kai ga shafe makonni uku ana mummunar faɗa.

Sai dai Olmert ya ce min a lokacin, da zai zama abu mai sauƙi Abbas ya rattaɓa hannu kan yarjejniyar.

Daga nan idan Firaministan Isra'ila na gaba ya yi yunƙurin soke ta, '' Zai iya faɗawa duniya cewa rashin nasarar daga Israi'la ce''.

Rafiq Husseini
Bayanan hoto, Rafiq Husseini, Shugaban ma'aikatar fadar shugaban Falasɗinawa ya bayyana Olmert a matsayin mutumin da bai yi nasara ba

Jim kaɗan bayan nan zaɓen Isra'ila ya biyo baya a Fabrairu.

Ɗan jam'iyyar Likud, Benjamin Netanyahu, wanda ya yi ƙaurin suna wajen nuna adawarsa ga kafa ƙasar falasɗinawa mai cin gashin kanta, ya zama Firaminista.

Shirin Olmert da taswirarsa su ka zamo tarihi.

Tsohon Firaministan ya ce har yanzu ya na jiran amsar Abbas, sai dai shirinsa ya daɗe da shiga cikin dogon jerin damarmakin da aka rasa na kawo ƙarshen rikicin Israila da yankin Falaɗinu.

A shekarar 1973, tsohon jami'in diflomasiyya na Isra'ila ya ce Falasɗinawa '' ba sa taɓa rasa damar rasa wata dama''. Wannan wani kalami ne da jam'ian Isra'ila ke yawan maimaitawa a shekaru bayan nan.

Sai dai duniyar ta fi haka sarƙaƙiya, musamman tun bayan ɓangarorin biyu sun sanya hannu kan yarjejeniyar Oslo na 1993 mai cike da tarihi.

Amincewa da yarjejeniyar da akayi tare da musabaha a wani lambu da ke fadar White House tsakanin Yitzshak Rabi da Yasser Arafat ya nuna alamun fata mai kyau, duk da dai a ƙarshe ba ayi nasara ba.

Dalilin hakan na da sarƙaƙiya, kuma kowanni ɓangaren na da iya nasa laifin, sai dai a zahiri, tun farko ba a tsara abin yadda ya kamata ba.

Ni shaida ne kan wannan rashin jituwar shakara 24 da ta gabata.

A watan Janairun 2001, a wani wurin shaƙatawa a Masar mai suna Taba, masu sasantawa tsakanin Isra'ila da Falasɗinawa a wannan karon ma sun ga wata yarjejeniya da bata kai ga nasara ba.

Ɗaya daga ciki tawagar Falasɗinawa ya zana wata kwarya kwaryar taswira a kan tsumma kuma ya faɗa min cewa, a karon farko, su na kallon wannan a matsayin abin da zai iya zama ƙasar Falasɗinawa.

Sai dai maganganun ba su yi tasiri ba sakamakon rikicin da ake samu a kan titunan Gaɓar Yamma da Gaza inda aka samu boren Falasɗinawa karo na biyu wanda ya ɓarke a watan Satumban da ya gabata.

A wannan karon ma, Isra'ila na tsaka da miƙa mulki.

Firaminista Ehud Barak ya ajiye aiki. Ariel Sharon ya samu nasara kansa cikin sauƙi makonni kaɗan bayan hakan.

Kwarya kwaryar taswirar da aka zana a kan tsumma, kamar dai taswirar Olmert shekaru takwas bayan nan, na nuna hanyar da da ace an bi, za ta warware matsalar.