Messi ya ci kwallo na 800 a tarihinsa na taka leda

An wallafa

Lionel Messi ya ci kwallo na 800 a karawar da Argentina ta doke Panama 2-0, wasan farko tun bayan da ta lashe kofin duniya a Qatar a 2022.

Mai shekara 35 shine ya ci na biyun a bugun tazara, ya zama na biyu bayan Cristiano Ronaldo, wanda ke kan gaba a wannan bajintar ci kwallaye da yawa.

Messi ya ci kwallo 672 a kaka 17 da ya yi a Barcelona da 29 da ya zura a raga a Paris St Germain.

Haka kuma ya ci wa Argentina kwallo 99 har da biyun da ya ci Faransa a wasan karshe a kofin duniya a Qatar.

Messi ya ci Panama na biyu a bugun tazara a minti na 89 a karawar da suka yi a filin wasa na Monumental de Nunez Stadium a Buenos Aires.

Thiago Almada ne ya fara cin kwallo a minti na 11 da fara wasan.

Messi ya lashe manyan kofuna a tamaula a ciki har da Champions Leagues hudu da La Liga 10 da Copa America da kofin duniya.

Daya daga fitattun 'yan kwallo a duniya ya lasshe Ballon d'Or bakwai, ya haura Ronaldo mai biyar

Kofin da Messi bai dauka ba kawo yanzu shine French Cup a PSG, wadda aka fitar da ita a gasar bana.

Messi ya lashe kofi 35 a Barcelona, kungiyar da ya koma tun yana da shekara 13, wanda shine kan gaba a yawan yi mata tamaula mai 778 jimilla.

Ya kuma ci kwallo 474 ya bayar da 192 aka zura a raga, shine kan gaba a yawan cin kwallaye a kaka daya a La Liga mai 50 a raga a wasa 37 a 2011/12.

Shine kan gaba a La Liga a cin kwallo uku rigis sau 36, kuma ya yi kan-kan-kan da Ronaldo a cin kwallo uku rigis sau takwas a kaka daya.

Ronaldo ne kan gaba a zura kwallaye a Champions League mai 140, Messi yana da 129, dan kasar Argentina ne na farko da ya fara cin biyar a wasa a gasar zakarun Turai .

Kungiyoyin da Messi ya ci kwallaye da yawa

Kungiya. Yawan wasa Kwallaye

Sevilla 43 38

Atletico Madrid 43 32

Valencia 36 31

Athletic Bilbao 41 29

Real Betis 24 26

Real Madrid 47 26

Messi ne kan gaba a yawan buga wa Argentina wasanni mai 172, saura kwallo daya ya ci na 100 a kasar.

Gabriel Batistuta ne na biyu mai kwallo 56 a wasa 78 da ya yi wa Argentina.

Wadanda ke kan gaba a yawan ci wa tawaga kwallaye a duniya, sun hada Ronaldo a Portugal mai 120 da Ali Daei na Iran mai 109, sai Messi mai 99.