Ingila ta zama ta hudu a duniya

An wallafa

Tawagar kwallon kafa ta mata ta Ingila ta samu ci gaba inda ta zama ta hudu a jerin gwanayen hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa na wannan wata.

Tawagar ta samu wannan tagomashi ne da ta tsallake mataki hudu, bayan da ta yi nasarar cin kofin kasashen Turai na wannan shekara 2022.

Tawagar ta Sarina Wiegman ta doke takwararta ta Jamus, wadda ita kuma ta zama ta biyu a yanzu a duniya, a wasan karshe na gasar da ci 2-1 ta dauki babban kofinta na farko.

Amurka wadda daman ita ce ta daya a tsakanin tawagogin kwallon kafar na mata na duniya ta ci gaba da zama ta daya.

Afirka ta Kudu wadda ta ci kofin nahiyar Afirka na mata a watan da ya gabata ta tsallake mataki hudu inda yanzu ta zama ta 54 a duniya.

Zambia wadda ta kai wasan kusa da karshe a gasar ta Afirka ta tsallake mataki 23 inda yanzu ta zama ta 80 a duniya.

Brazil wadda ta ci kofinta na hudu na nahiyar Amurka na mata a watan Yuli ta ci gaba da zama ta tara.

Scotland ce ta 23, yayin da Wales take ta 30 Ireland ta Arewa kuwa ta 50, inda Jamhuriyar Ireland take ta 26.