Har yanzu West Ham na neman mai cin ƙwallaye

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

West Ham United na fama da karancin ƴan wasan da ke buga gurbin cin ƙwallaye, sai dai sabon koci, Graham Potter ya ce ba lallai sai sun shiga kasuwa ba.

Ƙungiyar ta doke Fulham ranar Talata a Premier League ba tare da Niclas Fullkrug da Jarrod Bowen da Michail Antonio da kuma Crysecio Summerville ba.

Saboda haka Potter sai ya yi amfani da Lucas Paqueta da kuma Tomas Soucek a karawar da Fulham, inda ƙwalliya ta biya kuɗin sabulu.

Kowannensu ya ci ƙwallo har da Carlos Soler a fafatawar da West Ham ta yi nasara da cin 3-2 a wasan farko na Potter a gida a Premier League.

To sai dai Potter ya fara da jan ragamar West Ham ranar Juma'a a FA Cup da Aston Villa ta kai zagaye na huɗu.

Potter tsohon kocin Brighton da Chelsea ya maye gurbin Julien Lopetegui, wanda ya kasa taka rawar gani a bana, tun bayan maye gurbin David Moyes.

An yi ta alakanta masu buga gurbin cin ƙwallaye da West Ham, ciki har da Evann Guessand na Nice da mai taka leda a RB Leipzig, Andre Silva.

Ranar Asabar West Ham za ta karɓi bakuncin Crystal Palace a wasan mako na 22 a Premier League.