Man United ta haɗo maki uku a gidan Fulham

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Manchester United ta yi nasara a kan Fuulham da cin 1-0 a Craven Cottage a wasan mako na 23 a Premier League ranar Lahadi.

United ta ci ƙwallon ta hannun Lisandro Martínez, saura minti 12 a tashi wasan a Craven Cottage.

United ta kara na biyu ta hannun Amad Diallo daf a tashi, amma ba a karɓa ba, saboda satar gida kamar yadda VAR ta fayyace.

Da wannan sakamakon United ta yi sama zuwa mataki na 12 da maki 29, ita kuwa Fulham mai maki 33 tana ta 10 teburin Premier League.

Wannan shi ne karo na tara da United ta kai ziyara Fulham, ta yi nasara ta takwas daga ciki da canjaras ɗaya.

Wasa na 19 a baya nan da suka fafata a tsakaninsu, inda Fulham ta ci ɗaya daga ciki da canjaras uku aka doke ta 15.

Haka kuma Fulham ta yi rashin nasara a gida a karon farko, bayan wasa na bakwai, wadda ta ci karawa biyu da canjaras huɗu da wannan rashin nasara.

Rabonda a doke Fulham a gida tun Nuwambar 2024, bayan da Wolverhampton ta doke ta 4-1 a Premier League.

Sabon kociya, Ruben Amorim ya yi rashin nasara shida daga wasa 12 da ya ja ragamar United, ba a taɓa doke ƙungiyarsa wasa sama da shida ba a duk kakar tamaula.

Wasannin da ke gaban United nan gaba shi ne Europa League da FCSB, sai Premier League da Crystal Palace da FA Cup da Leicester City.