Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Fifa Club World Cup: Man City da Chelsea na jiran rukunin da za su fafata
Manchester City da Chelsea za su san rukunin da kowacce za a saka ta ranar Alhamis, domin buga Fifa Club World Cup a Amurka a 2025.
City ta samu tikitin shiga gasar da za a yi tata ɓurza tsakanin ƙungiya 32 a baɗi, saboda lashe Champions League a 2023, ita kuwa Chelsea ta ɗauki na 2021.
Sauran manyan ƙungiyoyin da za su kara a wasannin har da Real Madrid da Bayern Munich da Paris St Germain.
Haka kuma ƙungiyar Kudancin Amurka, Boca Juniors da Flamengo suna daga cikin waɗanda za a kara da su a 2025.
Za a fara gasar daga 15 ga watan Yuni a Amurka har da ƙungiyar da Lionel Messi ke taka leda, Inter Miami.
To sai dai mahukuntan gasar Premier League na fargabar ko City da Chelsea za su samu kuzarin buga babbar gasar tamaula ta Ingila ta 2025/26, wadda za a fara ranar 17 ga watan Agustan 2025.
Rukuni huɗu daga takwas zai ƙunshi ƙungiyoyin Turai, sai dai an keɓe City da Chelsea daga cikin rukunin a wasannin.
Za a buga wasan karshe a filin MetLife a New Jersey ranar 3 ga watan Yulin 2025.