PSG na Harin Rashford, yayin da Liverpool za ta siyar da Ibrahima Konate

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Marcus Rashford
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Paris St-Germain na duba yiwuwar musayar ɗan wasanta mai shekaru 23 Bradley Barcola ga Manchester United don siyen ɗan wasanta Marcus Rashford, da ke masatyin ɗan wasan aro a Barcelona 28.

Ɗan wasa Sergio Reguilon, 28, da kwantaraginsa ya ƙare da Tottenham a kakar wassani, na dab da komawa Inter Miami in da za su haɗe da Lionel Messi. (Marca - in Spanish)

Manchester United ta ƙi amince wa da tayi da AS Roma ta yi mata kan siyen ɗan wasan Joshua Zirkzee, mai shekaru 24. (Corriere dello Sport - in Italian)

Har ila yau dai United, na na zsub siyar da Zirkzee don sake zuba kuɗi a siyo ƙarin wasu ƴan wasa a kakar cinikin ƴan wasa. (Metro)

Arsenal na harin ɗan wasan Lille mai shekaru 18 Ayyoub Bouaddi. (RMC Sport, via Teamtalk)

Liverpool za ta amince da tayin fam miliyan 15 wajen siyar da ɗan wasan Ibrahim Konate a watan Janeru idan suka sami wanda zai mayar ata gurbinsa. (Football Insider)

Babu wata tattaunawa tsakani ƙungiyoyi ƙwallo ƙafa na Saudiya da ɗan wasan Liverpool Mohammed Salah. (Fabrizio Romano)

An sanar da Tottenham cewar babu wani shiri da Samu Aghehowa ke yi na barin Porto in January. (Teamtalk)

Manchester United na iya fasa siyen dan wasa Christos Mouzakitis mai shekaru 18, inda ɗan wasan na Olympiacos ya fi sha'awar komawa taka leda a Real Madrid. Football Insider)