Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Bournemouth ta kafe a zawarcin Semenyo, Branthwaite zai sabunta kwantiragi da Everton
Gwiwar Manchester United da Newcastle da Tottenham ta yi sanyi a zawarcin ɗanwasan Ghana Antoine Semenyo mai shekara 25 yayin da Bournemouth ke neman fam miliyan 70 kafin cefanar da shi. (The I - subscription required)
Arsenal na fatan daidaitawa kan yarjejeniyar sayen ɗanwasan Sifaniya mai shekara 21 Cristhian Mosquera bayan tattaunawa da Valencia. (Guardian)
Ɗanwasan tsakiya na Kamaru Bryan Mbeumo mai shekara 25 ya sanar da Brentford da Tottenham kan matakinsa na ƙulla yarjejeniya da Manchester United a bazara. (The Athletic - subscription required)
Ɗanwasan Everton mai shekara 23 Jarrad Branthwaite ya shirya sabunta kwantiraginsa da shekara biyar yayin da kulob ɗin ke fatan ɗanwasan tsakiya na Senegal Idrissa Gueye mai shekara 35 zai sa hannu kan kwantiragin shekara ɗaya. (Times - subscription required)
RB Leipzig ya zama kulob na baya-bayan nan da ya bayyana sha'awar sayen ɗanwasan tsakiyar Ingila Harvey Elliott mai shekara 22, idan zai bar Liverpool a bazara yayin da Brighton da West Ham ke cikin masu zawarcinsa. (Mirror, external)
Ɗanwasan Feyenoord Antoni Milambo ya shirya zama ɗanwasan farko da Keith Andrew ya ɗauka a matsayin kocin Brentford yayin da ƙungiyar ke tattaunawa don ɗauko ɗanwasan na Netherlands mai shekara 20.
Leeds United ta soma tattaunawa da ɗanwasan Juventus da Brazil Douglas Luiz mai shekara 27 kan komawa ƙungiyar a wannan bazarar. (Calciomercato - in Italian, external)
West Ham na zawarcin ɗanwasan Amurka Yunus Musah mai shekara 22 daga AC Milan daidia lokacin da Nottingham Forest ke tattaunawa da tsohon matashin ɗanwasan na Ingila. (Tuttomercatoweb - in Italian, external)
Sai dai Forest ta haƙura da zawarcin ɗanwasan Juventus mai shekara 25 Timothy Weah bayan da ɗanwasan ya yi watsi da tayin ƙulla kwantiragi da kulob ɗin. Forest ta amince da yarjejeniyar kusan fam miliyan 19 da kulob ɗin na Italiya kan Weah da ɗanwasan Belgium Samuel Mbangula mai shekara 21. (ESPN, external)
Newcastle ta shirya ƙara kuɗi don sayen ɗanwasan Brighton Joao Pedro bayan da aka yi fatali da tayin fam miliyan 50 kan ɗanwasan na Brazil mai shekara 23. (Talksport)
Aston Villa na hamayya da Juventus da Lazio kan ɗanwasan Lens mai shekara 23 Neil El Aynaoui, da ke taka leda wa Morocco leda a matakin ƴan ƙasa da shekara 23. (Calciomercato - in Italian, external)
Ɗanwasan Crystal Palace Eberechi Eze na daga cikin ƴanwasan gaba da Arsenal ke zawarcin su yayin da ita ma Tottenham ke ƙyalla ido kan ɗanwasan Ingila mai shekara 26. (Sky Sports)