Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'An aikata kisan ƙare-dangi a Darfur'
BBC ta samu sabbin shaidu kan kisan ƙare dangin da aka yi a yammacin Sudan tun bayan yaƙin da ya ɓarke tsakanin manyan sojoji biyu da suka samu rabuwar kai a watan Afrilu.
Wani sharhi da aka yi sakamakon hotunan tauraron ɗan adam da kuma kafafen yaɗa labarai da bayanan da aka tattara ya kuma nuna yadda sojoji suka cinna wa wasu ƙauyuka akalla 68 wuta bayan fara yaƙin basasar ƙasar.
Ministan kula da harkokin Afirka na Birtaniya, Andrew Mitchell ya shaida wa BBC cewa wannan wani mummunan "kisan ƙare dangi ne".
Wannan ne karon farko da Gwamnatin Birtaniya ta yi amfani da irin wannan harshe domin bayyana abin da ke faruwa a Sudan.
Janar Abdel Fattah al-Burhan, wanda ke shugabantar ɗaya daga cikin tsagin da ke rikici a Sudan - ya shaida wa BBC cewa za su yi aiki tare da Kotun Duniya domin gurfanar da waɗanda suka aikata laifin.
Mafi yawan zarge-zargen da ake yi na laifukan yaƙi na ƙabilanci an fi alaƙanta su da mayaƙan da ke da ƙawance da dakarun RSF, waɗanda ke yaƙi domin karɓe iko da ƙasar.
Sai dai RSF ta sha musanta hannu a wannan aiki, kuma tana kira kan a gudanar da bincike mai zaman kansa na duniya.
Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta CIR, mai yaƙi da bayanan ƙarya ce ta gudanar da wannan bincike, kuma gwamnatin Birtaniya ce ke ɗaukar nauyin gudanar da ayyukan ƙungiyar, wadda ta riƙa samun hujjoji kan yaƙin na Sudan.
Ƙuyngiyar na amfani da na'urorin fasaha da ke gano inda aka cinna wuta.
Suna duba hotunan tauraron ɗan'adam donin gano inda hayaƙi ya tashi da kuma inda aka ƙona gine-gine.
Sun kuma yi daidai da bayanan da suka samu daga kafafen yaɗa labarai, wanda aka bi diddiginsu ta hanyar taswira da hotunan.
Wutar baya-bayan nan da aka gano an cinna, ita ce a ƙauyen da ake kira Amarjadeed, da ke kudancin Darfur, inda hotunan hukumar kula da sararin samaniya suka nuna alamun ƙona wuri tsakanin 18 ga watan Satumba zuwa 9 ga watan Oktoba.
A haka ƙungiyar CIR ta samu hujja kan yadda wata tawagar dakarun mayaƙa suka cinna wa ƙauyuka aƙalla tara wuta a ranar 16 ga watan Agusta.
Da fari sai da aka yi amfani da na'urar da take iya gano wuraren da aka sanya wa wuta.
Sannan ta yi amfani da hotunan tauraron ɗan adam don gane ko wutar na da alaƙa da wasu ƙauyuka da suka shahara.
CIR ta samu hotunan ta kafafen sada zumunta da aka samu daga yammacin Sudan da suka nuna mayaƙan na sanya wa ƙauyukan wuta, suna kuma sace musu hatsi a talabijin sun je wurin ne a kan babura.
Sun saurari abin da mayaƙan suke faɗa - suna kuma bincike kan kayan da suka sanya, domin ƙoƙarin gano su wane ne.
Wasu mayaƙan na sanye da wani farin awarwaro, wanda hakan ke nufin su mayaƙan ƙungiyar Larabawa ce ta Bani Halba, wadda ke da alaƙa da dakarun RSF.
An bibiyi wurin da aka ɗauki hotunan da aka wallafa a shafukan sada zumunta, kuma an iya ganin wasu duwatsu da wasu gine-gine da aka iya gane wa.
Duka waɗannan abubuwa an same su ne a rana ta farko da mayaƙan suka sanya wa ƙauyen Buro wuta, kafin daga baya su nufi arewaci su sanya wa Awsatabi wuta, kuma suka yi gabashi zuwa wasu ƙauyukan na daban.
"Girman abubuwan da muka iya tarawa sun fi girman abubuwan da muka gani a baya," in ji Ben Strick, daraktan binciken ƙungiyar CIR.
"Mun samu bayanan hare-hare 89, da suka yi sanadin ƙona ƙauyuka 68 tun ranar 15 ga watan Afrilu, wanda adadi ne mai yawa. A wasu ƙauyukan wasu gidaje aka ƙona, amma a wasu hare-haren ƙauyukan ne gaba ɗaya suka ƙone. Wanna abu ne mai tayar da hankali idan aka dubi illar da ya yi wa fararen hula''.
"Abin da ya faru cin zarafi ne, a ce na ƙona ƙauyuka ɗaya baya ɗaya , musamman a Darfur, inda a nan ne aka samu wani babban rikici a wajen Khartoum.''
Yankin ya kasance fagen daga tsakanin ƙungiyoyin Larabawa da ke adawa da juna, a wasu lokuta kuma Larabawa ne ke kai farmaki ga mutanen da ba Larabawa ba a yankin.
An tilasta wa Amin Yakubu da iyalansa barin Darfur bayan wani hari da 'yan tawayen Larabawa suka kai.
"Wata rana da safe bayan mun dawo daga sallar asuba, sai wani gurneti ya fashe, nan take wuyan abokina ya karye, abin da kuma ya yi sanadin mutuwarsa."
Ya yi ta gudu yana tsallake gawarwaki domin tsira da rayuwarsa, kuma har yanzu bai san inda 'yan uwansa suke ba. Yayin da yake yi wa BBC bayani a sansanin 'yan gudun hijira da ya samu isa a watan da ya gabata, ya ce rikicin ya zama na ƙabila, amma ya shafi kowa a yankin.
"A ranar da abin ya auku babu wanda ya iya yin bacci a yankin".
"Kowa na kwana ne a ƙasa duk tsawon dare, saboda harbe-harben bindiga. A yanzu, kowa ya fice daga ɗan ƙaramin garin namu, babu wanda ya saura a garin a iya sanina".
MDD ta damu
Shugaban shirin bayar da tallafi na Majalisar Dinkin Duniya a Darfur, Clementine Nkweta-Salami ya ce "yayin da wannan rikici ke yaɗuwa, muna samun rahotonnin ƙaruwar laifukan fyaɗe da cin zarafin jinsi, da ɓatar da mutane, da tsare mutane ba bisa ƙa'ida ba tare da sauran laifukan take haƙiƙin ɗan'adam da ƙananan yara.
Manufar cibiyar bincike ta CIR da ke London shi ne tattara hujjojin da wata rana za a iya gurfanar da waɗanda ke da hannu a rikicin gaban shari'a. Shafinsu na intanet na cike da bayanan abinda suka gano, kuma ana sabunta shi a kowane lokaci.
A hirar da ya yi baya-bayan nan a birnin New York, Janar Burhan ya shaida wa BBC cewa zai goyi bayan duk wani ko wata ƙungiya da za ta taimaka wajen gurfanar da duk mutanen da ya bayyana da "masu babban laifi" a gaban shari'a.
"Muna jin taƙaici kan irin halin da 'yan Sudan ke ciki a duk inda suke, ko Darfur ko Khartoum ko ma a ina suke matuƙar wannna rikici ya shafe su".
"Muna da burin haɗa kai da kowa, ko da Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya ce. za mu haɗa kai da ita domin gurfanar da wadanda ke da hannu wajen aikata wannan laifi".
Aƙalla mutum 7,000 ne aka kashe tun bayan fara yaƙin.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce fiye da mutum miliyan biyar ne aka tilasta wa barin gidajensu, yayin da dama suka fice daga ƙasar.
MDD ta kuma ce kimanin rabin al'ummar ƙasar ne ke cikin yanayin buƙatar tallafi.
Akwai fargabar cewa rikicin zai yadu zuwa makwabtan ƙasashe tare da ƙara zaman ɗar-ɗar a yankin.
Haka kuma akwai damuwa kan ƙara dagulewar rikicin, sakamakon rahotonnin da ke cewa ƙasar Haɗaɗdiyar Daular Larabawa na bai wa RSF makamai, wani abu da jami'ar UAE din suka musanta.