Real Madrid na farautar Branthwaite, Neymar na son komawa Barcelona

Jarrad Branthwaite

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Real Madrid ta matsa ƙaimi kan ɗan wasan tsakiya a Everton da Ingila, Jarrad Branthwaite mai shekara 22. (Teamtalk)

Ƙungiyar Napoli ta Serie A na shirin gabatar da tayi kan ɗan wasan Denmark, Rasmus Hojlund daga Manchester United, idan ƙungiyar ta Firimiya za ta karbi fam miliyan 72 kan matashin mai shekara 22. (Talksport)

Manchester City na son saye ɗan wasan Newcastle da Ingila, Tino Livramento, mai shekara 22, da kuma mai bugawa Juventus tsakiya, Andrea Cambiaso, mai shekara 25, a kokarin kimtsawa sabuwar kaka. (Telegraph - subscription required)

Za a tuntubi ɗan wasan gaba a Ingila, Cole Palmer, mai shekara 22, kan ko zai cigaba da zama a Chelsea ko da kuwa sun rasa damarsu ta gasar zakarun Turai. (Times - subscription required)

Atletico Madrid na son saye ɗan wasan tsakiya a Croatia, Mateo Kovacic, mai shekara 30 daga Manchester City a wannan kaka. (Caught Offside)

Ƙungiyoyi na son amfani da matsalar kudi da Manchester United ke ciki wajen cinikin 'yan wasanta. (Telegraph - subscription required)

Babu ƙungiyar da ta nuna sha'awar ɗaukar ɗan wasan tsakiya na Brazil, Casemiro da ke taka leda a Manchester United. (Teamtalk)

Ƙungiyar MLS ta San Diego ta gaggara daidaitawa kan saye ɗan wasan tsakiya na Belgium, Kevin de Bruyne daga Manchester City a wannan kaka. (Teamtalk)

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ɗan wasan Southampton mai shekara 19, Tyler Dibling zai bar ƙungiyar idan suka fada rukunnin dagaji a Firimiyar Ingila.(Football Insider)

Tottenham na iya rabuwa da ɗan wasan tsakiyan Mali, Yves Bissouma, mai shekara 28, idan aka buɗe kasuwar cinikin ƴan wasa a bazara. (Give Me Sport)

Newcastle United za ta saurari tayi kan mai tsaron raga na Ingila, Nick Pope mai shekara 32, a wannan kaka. (Football Insider)

Neymar ya koma ƙungiyarsa ta farko Santos amma wakilinsa Pini Zahavi ya ce ɗan wasan na Brazil mai shekara 33, na iya sake komawa Barcelona a bazara mai zuwa. (Sport - in Spanish)

Manchester United na son cimma matsaya da ɗan wasan Sporting, Geovany Quenda, mai shekara 17, kafin a bude kasuwar cinikin ƴan wasa ta bazara. (Give Me Sport)

Koci Ruud van Nistelrooy na fuskantar matsin lamba daga Leicester City. (Football Insider)

Shugaban Newcastle United, Yasir Al-Rumayyan ta kai ziyara birnin domin yanke hukunci karshe kan shirin da suke da shi na gina filin wasa. (Sun)