Arsenal na son Kimmich, Aston villa ta bi sahun masu farautar Vlahovic

Joshua Kimmich

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Arsenal na son sayen ɗan wasan tsakiya a Bayern Munich da Jamus, Joshua Kimmich, mai shekara 30 a lokacin bazara. (Sky Sports)

Ƙungiyar ta nuna matsuwa sosai wajen ganin ta mallaki Kimmich, yayinda take yarjejeniyar sayo ɗan wasan tsakiya Martin Zubimendi, mai shekara 26, daga Real Sociedad. (Metro)

Liverpool da Barcelona na cikin ƙungiyoyin da ke zawarcin Kimmich. (Sun)

Aston Villa ta bi sahun Arsenal a farautar ɗan wasan Serbia, Dusan Vlahovic mai shekara 25, wanda ake ganin zai bar Juventus a lokacin bazara. (TeamTalk)

Liverpool na shirin sayo 'yan wasan baya a wannan kakar a kokarin daina dogaro da ɗan wasan Netherlands da baa san makomarsa ba Virgil van Dijk, yayinda shi kuma ɗan wasan Ingila, Trent Alexander-Arnold mai shekara 26, ke shirin barin ƙungiyar zuwa Real Madrid. (Football Insider), external

Liverpool za ta iya bada dama ɗan wasanta na Colombia, Luis Diaz ya tafi a kan yuro miliyan 70, yayinda Atletico Madrid ke matsa ƙaimi kan matashin mai shekara 28. (Fichajes - in Spanish)

Chelsea ba ta da niyyar sayar da mai tsaron ragarta a lokacin bazara, duk dacewa ta nuna zawarcinta kan ɗan wasan Sifaniya, Robert Sanchez mai shekara 27, da kuma Filip Jorgensen na Denmark mai shekara 22. (Times - subscription required)

Arsenal na iya yanke hukuncin farautar ɗan wasan RB Leipzig mai shekara 21 daga Slovenia, Benjamin Sesko idan ta rasa ɗan wasan Newcastle United Alexander Isak ta Liverpool ke bibiya. (Liverpool Echo)

Newcastle ba ta da niyyar sauraron tayi kan ɗan wasanta mai shekara 22, Tino Livramento da Manchester City ke zawarci. (Football Insider)

Ɗan wasan Manchester United da Brazil, Casemiro mai shekara 33, na cikin 'yan wasan da AC Milan ke hari a lokacin bazara. (Fichajes - in Spanish)

Arsenal za ta fuskanci kalubale daga AC Milan kan ɗan wasan Wolves da Aljeriya, Rayan Ait-Nouri mai shekara 23. (CaughtOffside)

Everton ba ta da niyyar tabbatar da zaman ɗan wasan Leeds United, Jack Harrison mai shekara 28, da ke zaman aro a ƙungiyarta. (Football Insider)