Barca ta kai daf da karshe bayan kaka shida a Champions League

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Barcelona ta kai daf da karshe a Champions League a karon farko bayan kaka shida, sakamakon doke Borussia Dortmund 5-3 gida da waje.

Dortmund ta ci Barcelona 3-1 ranar Talata a Jamus, wadda ta sha kashi 4-0 a wasan farko a kwata fainal a Sifaniya a gasar ta zakarun Turai.

To sai dai Dortmund ta taka wa Barca burki, wadda ta yi wasa 24 a jere ba tare da rashin nasara ba da yin canjaras huɗu daga ciki a dukkan fafatawa.

Rabon da Barca ta yi nasara tun 2-1 da Atletico Madrid ta yi nasara a cikin watan Disambar 2024, kenan tun da aka shiga 2025 ba a ci Barcelona ba.

Rabon da Barcelona ta kai daf da karshe a gasar zakarun Turai tun 2019 a hannun Liverpool, kenan tana kishirwar lashe kofin kakar nan.

Wannan shi ne karo na bakwai da Barcelona ke nisa a gasar ta zakarun Turai, kuma a wasan bakwai ta kai zagayen karshe.

Sai dai karo tara tana kasa zuwa daf da karshe a gasar ta zakarun Turai a tarihi.

Ga jerin wasannin da ta buga a irin wannan lokacin:

- European Cup 1959/60 da Real Madrid (an ci Barca 2-6)

- European Cup 1960/61 da Hamburg (Barca ta ci 1-0 ).

- European Cup 1974/75 da Leeds (an ci Barca 2-3)

- European Cup 1985/86 da Göteborg (Barca ta yi nasara a fenariti)

- Champions League 1993/94 da Porto (Barca ta ci 3-0 a Camp Nou)

- Champions League 1999/00 da Valencia (an ci Barca 3-5)

- Champions League 2001/02 da Real Madrid (an ci Barca 1-3)

- Champions League 2005/06 da Milan (Barca ta yi nasara 1-0)

- Champions League 2007/08 da Manchester United (an ci Barca 0-1)

- Champions League 2008/09 da Chelsea (Barca ta kai zagayen gaba)

- Champions League 2009/10 da Inter (an ci Barca 2-3)

- Champions League 2010/11 da Real Madrid (Barca ta yi nasara 3-1)

- Champions League 2011/12 da Chelsea (an ci Barca 2-3)

- Champions League 2012/13 da Bayern (an ci Barca 0-7)

- Champions League 2014/15 da Bayern (Barcelona ta yi nasara 5-3)

- Champions League 2018/19 da Liverpool (an ci Barca 3-4)

A 1991/92 babu zagayen daf da karshe, inda Barcelona ta kai karawar karshe kai tsaye, bayan da ta yi ta ɗaya a rukunin da ya haɗa da Sparta Prague da Benfica da kuma Dinamo Kyiv.

Barcelona tana da Champions League biyar, wadda rabon ta da kofin tun 2015, bayan doke Juventus 3-1.