Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ta yaya yaƙin Isra'ila ke shafar tattalin arziƙin ƙasar?
- Marubuci, Jeremy Howell
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 5
A cikin shekara ɗaya da ta gabata, Isra'ila ta tura dubban dakaru zuwa Gaza da kudancin Lebanon tare da kai dubban hare-hare ta sama a kan abokan gabarta, sannan ta kashe miliyoyin dala wajen amfani da babbar garkuwarta ta sama wajen kare makamai masu linzami da ƙananan jiragen sama marasa matuƙa na yaƙi da ake harba mata.
Gwamnatin Isra'ilar ta yi ƙiyasin cewa yaƙe-yaƙen da take yi da Hamas da Hezbollah ka iya ci mata sama da dala biliyan 60. Kuma tuni ma abin ya shafi tattalin arziƙin nata.
Nawa Isra'ila ke kashewa a yaƙe-yaƙenta?
Ministan kuɗi na Isra'ila, Bezalel Smotrich ya gaya wa majalisar dokokin ƙasar (Knesset ) a watan Satumba na wannan shekara ta 2024, cewa: "Muna cikin yaƙi mafi tsada da kuma tsawo a tarihin Isra'ila,'' kuma ya ƙara da cewa yaƙin zai iya cin tsakanin dala biliyan 54 da zuwa 68.
Ruwan bama-bamai da Isra'ila ke yi wa Lebanon, da kutsen da sojinta ke yi a kudancin ƙasar - haɗi da makamai masu linzamin da ta harba domin kawar da hare-haren sama da Iran take kai mata - za su ci gaba da ƙara yawan kuɗin da take kashewa.
Dakta Amr Algarhi, masanin tattalin arziƙi a jami'ar Sheffield Hallam da ke Birtaniya, ya ce, bayan faɗaɗa yaƙin, kuɗin ka iya ƙaruwa zuwa dala biliyan 93, idan yaƙin ya ci gaba har zuwa ƙarshen 2025.
Wannan ya zama kusan daidai da kashi ɗaya bisa shida na arziƙin da Isra'ila ke samu a shekara a cikin gida - wanda shi ne dala biliyan 530.
Ta yaya Isra'ila ke samun kuɗin da take kashewa a yaƙe-yaƙen?
Babban bankin Isra'ila na ta sayar da takardun laumi - inda yake ta karɓar bashi domin gudanar da yaƙin.
A tashi ɗaya a watan Maris na wannan shekara 2024 kaɗai, bankin ya samu dala biliyan 8 daga sayar da takardun lamuni.
Isra'ila na sayar da takardun lamuninta ne a cikin ƙasar da kuma waje, inda take sayar da takardun ga Yahudawan da ke wajen ƙasar.
Bayanai daga Babban Bankin na Isra'ila na nuna cewa 'yan ƙasashen waje ba sa sha'awar sayen takardun lamuni na Isra'ilar.
Bankin ya ce kashi 8.4 cikin 100 ne na takardun aka sayar a waje idan aka kwatanta da kashi 14.4 da aka saya a watan Satumba na 2023 - wata ɗaya kafin fara yaƙi da Hamas.
“Wannan ya sa gwamnati ta ƙara yawan kuɗin ruwan da za ta bayar a kan takardun lamuninta, domin hakan zai sa 'yan ƙasashen waje su yi kwaɗayin saye,” in ji Farfesa Manuel Trajlenberg, masanin tattalin arziƙi a jami'ar Tel Aviv.
“Wannan ya sa kenan akwai ƙarin kashi 1.5 cikin ɗari na kuɗin da gwamnatin Isra'ila za ta biya na bashin takardun lamunin.” In ji masanin.
Haka kuma manyan hukumomin duniya uku da ke auna ƙarfin biyan bashi na gwamnatoci da kamfanoni na duniya - Moody’s, da Fitch da Standard and Poor’s – dukkaninsu sun nuna cewa matsayin gwamnatin Isra'ila na iya biyan bashi ya ragu tun farkon watan Agusta na 2024.
Hukumomin ba su fito fili sun ayyana ainahin alƙaluman raguwar ƙarfin biyan bashin na gwamnatin Isra'ila ba saboda suna ganin ba za ta iya biyan lamunin ba, in ji Dakta Tomer Fadlon na cibiyar nazarin tsaron ƙasa da ke Tel Aviv.
Ya ce babu wata matsala tattare da harkokin kuɗin gwamnatin Isra'ila.
Matsalar kawai ita ce, a cewarsa: “Hukumomin bayyana ƙarfin biyan bashin dukkanninsu a rahotonsu sun ce suna da fargaba a kan rashin wani tartibin tsarin kuɗi daga gwamnatin na yadda za ta iyatafiyar da kashe-kashen kuɗinta zuwa shekara ta 2025.”
Farfesa Karnit Flug, masaniya a kan tattalin arziƙi a cibiyar nazarin dumukuraɗiyya ta Isra'ila, kuma tsohuwar gwamnar Babban Bankin Isra'ila, ta ce gwamanti na tunanin zaftare dala biliyan 9.9 a kasafin kuɗinta tare da ƙara haraji domin ta cike giɓin kasafin kuɗinta.
Sai dai ta ce ana tsammanin gwamnati ta fuskanci tirjiya daga ƙungiyoyin ƙwadago da wasu daga cikin mambobin gwamnatin haɗaka, a kan wasu daga cikin tsare-tsaren nata.
Masana tattalin arziƙi da dama na kira ga gwamnati ta wallafa kasafin kuɗinta na 2025 yanzu, da tartibin tsarin tsimin da za ta yi ta magance yawan kuɗin da take kashewa a ayyukan soji.
Wane tasiri yaƙin ya yi kan tattalin arziƙin Isra'ila?
Tattalin arziƙin Isra'ila ya kasance yana bunƙasa sosai, har zuwa watan Oktoba na 2023, inda ya ragu sosai bayan ɓarkewar yaƙin.
Tsawon wannan shekara yawan kuɗin da ƙasar ke samu a cikin gida ya ragu da kashi 0.1 cikin ɗari, kamar yadda Bankin Duniya ya nuna.
Babban Bakin Insra'ila ya yi hasashen cewa a cikin wannan shekara ta 2024, tattalin arziƙin ƙasar zai ƙaru da kashi 0.5 cikin ɗari kawai.
Wannan shi ne hasashe mafi muni da bankin ya yi saɓanin na watan Yuli da ya yi, inda a lokacin ya ce tattalin arziƙin zai bunƙasa da kashi 1.5 cikin ɗari a 2024.
A cikin shekarar da ta gabata, kamfanoni da dama a Isra'ila ba su da isassun ma'aikata, abin da ya taƙaita yawan aikin da za su iya yi.
Wannan ya kasance ne saboda hukumomin sojin Isra'ilar sun kira sama da mutum 360,000 da ke zaman sojin kar-ta-kwana a farkon rikicin da Hamas.
To amma tuni sun kammala aiki ta sallame su, amma kuma ta gayyato wasu 15,000 domin taimaka mata a kutsen da take yi na ƙasa yanzu a Lebanon.
Haka kuma gwamnatin ta hana Falasɗinawa ma'akata kusan 220,000 daga Gaza da kuma Gaɓar Yamma shiga Isra'ila su yi aiki saboda dalilan tsaro.
Wannan ya shafi musamman ɓangaren gine-gine, wanda ke ɗaukar Falasɗinawa waje 80,000 aiki.
A yanzu ana ƙoƙarin ɗaukar wasu dubban ma'aikatan domin maye gurbin, daga ƙasashe irin su Indiya da Sri Lanka da Uzbekistan.
Farfesa Flug ta ce sakamakon raguwar bunƙasar tattalin arziƙin na Isra'ila a lokacin yaƙin, akwai yuwuwar ya yunƙuro ya bunƙasa sosai, da an kammala yaƙin - saboda ta wani fannin fasahar da ƙasar ke da ita a fannin kayayyaki.
Sai dai kuma ta ce saboda yaƙin ya fi duk na baya daɗewa kuma ya shafi al'ummar ƙasar da yawa, hakan ka iya sa tattalin arziƙin ya ɗauki lokaci mai tsawo kafin ya bunƙasa, kuma ma sannu a hankali.