Ɗanwasan Najeriya Iwobi na so ya ƙarfafa gwiwar matasa da waƙoƙinsa

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Fitaccen ɗanwasan Najeriya da ƙungiyar Fulham ta Ingila, Alex Iwobi ya ce harƙoƙin waƙa da ya fara zai taimaka masa wajen ƙarfafa gwiwar matasa.

A bana na ɗanwasan na fara waƙoƙin gambara, inda kwanakin baya ya saki waƙarsa ta biyu mai suna 'What's Luv?'

Waƙarsa ta farko ita ce Don't Shoot a watan Yuni, wadda aka saurara sau 60,000 a manhajar Spotify.

A cewarsa, "lokacin da nake tasowa a London, wasu daga cikinmu sun fuskanci ƙalubale da yawa.

"Ina fata waƙoƙin da nake yi za su ƙarfafa gwiwar wasu domin su samu nasara a duk abubuwan da suka a gaba."

A kakar bana an fara dukkan wasannin tara na Fulham a gasar Premier League.

Ya ƙara da cewa waƙoƙi ba sa ɗauke masa hankali daga taka leda. "Ina amfani da lokacin hutun da na samu ne domin yin waƙoƙi," in ji shi.