Yadda ma’aikatan lafiya ke bi ƙauye-ƙauye domin duba marasa lafiya a Kano
Yadda ma’aikatan lafiya ke bi ƙauye-ƙauye domin duba marasa lafiya a Kano
An wallafa
Tun da asuba ayarin motoci dauke da jami’an lafiya ke shiga karkara domin bayar da kiwon lafiya ga mutanen kauyukan da suke da nisa da birane ko kuma ba su da asibiti.
Ayarin jami’an lafiyar kan yi shela sannan daga bisani su yi sansani a kofar gidan mai unguwa ko dagaci inda a nan ne jama’a za su taru domin karbar magani.
Jihar Kano dai ta fito da tsarin bi gari-gari da motoci dauke da ma’aikatan lafiya da magunguna domin rage cunkoso a asibitocin birane da kuma kai wa jama’a kiwon lafiya har garuruwansu.



