Yaushe Real Madrid za ta gama cin moriyar Benzema?

Karim Benzema

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Ranar 12 ga watan Agusta, za a fara gasar La liga ta 2022/23, inda Real Madrid za ta kare kofin da ta dauka a kakar da ta wuce.

Real Madrid ce ta dauki kofin babbar gasar tamaula ta Sifaniya da kuma na Zakarun Turai, wato Champions League.

Karim Benzema dan kwallon tawagar Faransa, shi ne kan gaba a taka rawar gani da Real Madrid ta dauki La Liga na 35 da Champions League na 14 jumulla.

Dan wasan shi ne ya lashe kyautar takalmin zinare a matakin wanda yafi cin kwallaye a La Liga da Champions League a kakar da aka kammala.

A bana Real za ta fuskanci kalubale, bayan da Barcelona ta dauko 'yan wasa da yawa ciki har da Robert Lewandowski daga Bayern Munich.

Sauran kungiyoyin da za su buga kakar bana, duk sun daura damar yadda za su taka rawar gani a kakar nan, domin kwalliya ta biya kudin sabulu.

Benzema ya kai shekara 34 da haihuwa kawo yanzu, ko yaushe ne Real za ta dauko madadin dan kwallon?

Ga Mohammed Abdu da ya hada wannan rahoton

 

Karim Benzema

Asalin hoton, Real Madrid

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ranar 1 ga watan Yulin 2009 aka sanar da cewar Lyon ta cimma yarjejeniyar sayar da Karim Benzema ga Real Madrid.

Kudin cinikin ya kai yuro miliyan 35, idan aka hada da tsarabe-tsarabe ya kai yuro miliyan 41 jumulla.

Ranar 9 ga watan Yuli likitoci suka kammala auna koshin lafiyar dan kwallon, sannan ya saka hannu kan yarjejeniyar kaka shida a yammacin ranar a Real Madrid.

A kuma ranar aka gabatar da Benzema gaban magoya baya a Santiago Bernabeu, kamar yadda aka yi wa Kaka da Cristiano Ronaldo a kakar.

Benzema ya fara buga wa Real Madrid tamaula ranar 20 ga watan Yulin 2009 a karawar sada zumunta ta Shamrock Rovers a Dublin.

Shi ne ya ci kwallo tilo da ya bai wa Real Madrid nasarar 1-0 a minti na 87 a karawar da ya canji dan wasa, daga nan sai tarihi.

Kawo yanzu Benzema ya buga La Liga karo 415 da cin kwallo 219, shi ne na uku a yawan zazzaga kwallaye a raga a tarihin gasar, bayan Raul, mai 228 da Cristiano Ronaldo, mai 312 a raga.

Haka kuma dan kwallon tawagar Faransa ya buga wa Real Madrid wasa 123 a Champions League da cin kwallo 74.

Bayan da Real Madrid ta lashe La Liga da Champions League a bara - Benzema ya karbi kyautar takalmin zinare a kan gaba a cin kwallaye a gasar biyu.

Kwallo 27 ya zura a raga a La Ligar da ta wuce da tazarar tara tsakaninsa da na biyu, sannan ya ci 15 a Champions League.

Cikin kwallo 15 da Benzema ya zura a raga a kakar da aka kammala 10 daga ciki tun daga zagaye na biyu ya dunga ci, biyar a karawar cikin rukuni.

Dan wasan ya ci Paris St-Germain da Chelsea kwallo uku rigis kowacce, sannan shi ne ya ci Manchester City kwallon da ya kai Real karawar karshe.

Zaman Benzema a Real Madrid ya sa kungiyar ba ta yi jimamin tafiyar Cristiano Ronaldo, kyaftin din tawagar Portugal ba, wanda ya yi mata bajinta a karo da yawa.

Kamar Benzema jira yake Ronaldo ya motsa, nan da nan dan kwallon ya ja ragamar Real Madrid, musammam a kakar da ta wuce, inda kungiyar ta lashe La Liga da Champions League.

Ya zama wajibi a jinjina wa Benzema a Real Madrid a kakar da ta wuce, wanda ya taka gagarumar gudunmawa a wasa 46 da cin kwallo 44 a dukkan fafatawa.

To sai dai kuma shekaru sun ja, Benzema ya kai shekara 34, wanda aka haifa ranar 19 ga watan Disambar 1987.

Kamar yadda jikin dan wasa yake da zarar ka kai shekara 30 da haihuwa kwazo raguwa yake, ka dunga jinya kenan, kungiya ba za ta samu yadda take bukata ba.

Musamman gurbin da Benzema ke bugawa ana bukatar kazar - kazar da cin kwallaye, idan ka kasa daga nan ne za a ga baraka, shi ya sa koda yaushe dan kwallon Faransa ke iya kokarinsa a wasannin Real Madrid.

Gurbin mai tsaron raga shi ne koda shekarunka sun ja ba lallai ka kasa kwazo ba, domin baya bukatar guje-guje, illa tsare raga da aka iyakance wurin da gola zai tsaya.

Ya kamata tun yanzu Real Madrid ta yi tunanin wanda zai maye gurbin Benzema nan gaba, kamar yadda dan kwallon Faransa ya taka rawar gani a bara ba lallai bane ya yi kokari a bana ba.

Idan ka duba yadda Barcelona, wadda ta shiga matsin tattalin arziki a bara, amma a bana ta dauko ‘yan wasa biyar ciki har da Robert Lewandowski da Raphinha.

Karim Benzema

Asalin hoton, Getty Images

Wannan zai nuna maka cewar Barca ta farka daga baccin da ta yi, ba za ta bari Real ta yi abin da ta yi a kakar da ta wuce ba, sun fara El Clasico a Amurka a bana, inda Raphinya ya ci Real Madrid.

To sai da alama ta nuna cewar Real din ba ta yi shirin daukar mai cin kwallo ba kan fara kakar nan, watakila sai a watan Janairu idan taga baraka,

Koda Real Madrid za ta dauko mai cin kwallo matashi za ta saya, wanda za ta mora shekara da yawa, kamar yadda kwalliya ke biyan kudin sabulu tun da ta dauki Benzema.

Ko can baya Real ta kwan da sannin cewar ya kamata ta dauki mai cin kwallaye a matakin ko-ta-kwana, sai dai Mariano Diaz da Luka Jovic da kuma Borja Mayoral duk sun kasa yin abinda ake bukata.

Kawo yanzu Jovic ya bar Real, haka Marriano na kan hanya, yayin da Mayoral ya sa hannu kan komawa Getafe da taka leda.

Hakika Real Madrid ba ta bukatar wadan nan matasan, domin sun gaza, sun kuma kasa samar da abinda ake bukata, sannan ba su da makoma a kungiyar.

Karim Benzema

Asalin hoton, Getty Images

Real Madrid ta sani cewar Benzema ya kai shekara 34, zai iya jin rauni da ba a fatan yin jinya mai tsawo.

Ko a kakar da ta wuce a kwai wasan da Real kan kasa cin kwallo saboda rashin dan kwallon tawagar Faransa.

Kakar bana da za a fara cikin watan nan na Agusta za ta yi zafi matuka, domin kungiyoyi da dama sun yi cefane don ganin sun taka rawar da ta dace.

Dole ka tanadi ‘yan wasa masu kwarewa da koshin lafiya da za su buga kakar bana don a samu nasarorin da kungiya ke bukata.

Bayan La Liga da kungiyoyin za su buga ga Copa del Rey ga Champions League, sannan yan wasan da kake da su za su buga kofin duniya a bana a Qatar.

Wasu rahotanni na cewar Real Madrid ta farga tana neman matashin dan wasa mai shekara 17, Enrique Herrero daga Eintracht Frankfurt, domin ta yi reno.

Tsohon dan kwallon Villarreal ana hasashen daya ne daga cikin matasan da ke kan gaba a cin kwallaye a nahiyar Turai, wanda Barcelona da Chelsea ke kokarin dauka.

Haka kuma ana alakanta Real Madrid da wani matashin mai shekara shekara 17, Iker Bravo, dan kwallon matasan Sifaniya mai taka leda a Jamus.

Tsohon dan kwallon La Masia, Bravo ya koma Bayer Leverkusen a 2021, yanzu kuma Real Madrid na son daukar dan kwallon.

Duk da cewar matasa ne, Real Madrid za ta mori ‘yan kwallon nan gaba, ganin sun nuna kansu a gurbin cin kwallaye kuma nan gaba kadan za su iya fara gasar La Liga.

Tuni Brazo ya fara taka leda a Bundesliga.

Da yake a cikin watan nan za a fara gasar La Liga za mu sa ido mu gani kan kwazon da Real Madrid za ta yi, ko kofi nawa za ta dauka a kakar nan.

Ko Benzema zai haskaka a bana duk da Lewandowski da zai buga La Liga a kakar nan.

Duk wani kokarin Real Madrid za a auna shi ne da kwazon bara da ta dauki La Liga da Champions League - kasa da wannan bajintar za a auna Real da rashin kokari.

Haka shi kansa Benzema, zai ci kwallaye da yawa a kakar nan? ko zai kara lashe kyautar takalmin zinare a La Liga da Champions League - Ko zai ci kwallo da yawa fiye da wadanda ya zura a raga a kakar da ta wuce?

A karshen kakar nan idan da tsawon rai za mu samu dukkan wadan nan amsoshin.