Yadda ake kashe tsofaffi a Kenya da sunan maita

    • Marubuci, Njeri Mwangi a yankin Kilifi da Tamasin Ford a Landan
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Africa Eye
  • An wallafa

Sashen binciken ƙwaƙwaf na BBC Africa Eye ya binciko wani labari mai firgitarwa, da ke nuna yadda ake kashe tsofaffin da ake zargi da maita a lardin Kilifi na ƙasar Kenya. Sashen ya bankaɗo dalilan da suka sanya ake samun hakan.

Tambala Jefwa mai shekara 74, na zaune, yana kallon matarsa Sidi da ragowar idonsa ɗaya, yayin da take cire masa riga.

“Sun daɓa masa wuƙa a nan, sannan suka cire ta'' Inji Sidi, yayin da take nuna wajen da aka ji masa ciwo daga ƙasan kafaɗar sa.

Ta kuma ɗago kansa da hannuwanta, tana nuni da abin da ya faru da shi a wani harin na daban. ''Sai da aka yi masa ɗinki a nan saboda girman ciwon da ya ji''

Sau biyu ana zargin Mr Jefwa da maita, a garinsu mai nisan kilomita 80 daga garin Malindi da ke gaɓar teku. A harin farko an cire masa ido ɗaya, a na biyun kuma an kusa kashe shi.

Ma'auratan suna da gidan gona mai faɗin kadada 30, inda suke noma Masara da kuma kiwon Kaji. Suna da yaƙinin cewa rikicin da aka samu tsakanin su da sauran ƴan uwansu a kan filaye ne ya sa aka kusa kashe Mr Jefwa, ba wai zargin sa da maita ba kamar yadda aka yi iƙirari.

“An bar ni in mutu cikin jini. Na zubar da jini mai yawan gaske. Ban san me ya sa suka kai mani hari ba, amma babu shakka yana da alaƙa da rikicin filaye'' inji Mr Jefwa.

Akwai ƙasashe da yawa da mutane suka yarda da maita da sauran camfe-camfe.

Amma a wasu sassan Kenya da Malawi da Tanzaniya da kuma Afirka ta Kudu, ana iya amfani da wannan a matsayin wata hanya ta goyon bayan kisan mutanen da suka tsufa domin cinye filayen da suka mallaka.

Wani rahoto da ƙungiyar kare haƙƙin ɗan'adam ta Kenya ta fitar ya ce a kowanne mako ana kashe tsoho ɗaya a lardin Kilifi, da sunan maita. Jami'in ƙungiyar, Julius Wanyama ya ce iyalai sun gamsu cewa daga cikin gida ne ake samun wani da ke sanyawa a aikata kisan da sunan maita.

Ya ce: “Suna amfani da zancen maita a matsayin wata hanya ta samun hujja da goyon baya daga al'umma. Kuma sauran jama'a sai su ce idan dai maye ne to ya fi kyau a kashe shi kawai kowa ya huta''.

Mutane ƙalilan ne suke da cikakkun takardun mallakar fili a wannan ɓangare na duniya. Kuma hakan ya sa ana jira ne kawai su mutu ƴan'uwa su ci gado.

Mista Wanyama ya ce bakwai daga cikin goma na irin waɗannan kashe-kashe, tsofaffi ne maza ake kashewa, waɗanda suka mallaki filaye ko kuma ƙarfin ikon rabon gado yake a hannun su.

“A bisa tarihi, mutanen yankin Kilifi ba su damu da takardun shaidar mallakar filaye ba. Shaidar baki kawai suka dogara da ita, wadda kuma tsofaffin da ake kashewa ne suke bayar da irin wannan shaida. Saboda haka ne ake kashe mafi yawan su, domin idan aka kashe su shi ke nan an kawar da duk wata barazana game da mallakar fili,'' In ji Mista Wanyama.

An buɗe wata cibiyar kula da tsofaffi a wani waje mai nisan tafiyar ƴan sa'oi daga gidan Jefwa, kuma gidauniyar Malindi District Association ce ta kafa ta.

Cibiyar tana kula da tsofaffi aƙalla 30 waɗanda aka taɓa yunƙurin kashewa kuma yanzu suka gaza komawa gidajensu.

Katana Chara mai shekara 63, wanda idan ka ganshi za ka ɗauka shekarunsa sun fi haka ya shafe kusan watanni 12 yana zaune a cibiyar.

Ya koma cibiyar ne bayan harin da aka kai masa da adda, inda aka bi shi har cikin ɗakinsa, a cikin watan Afirilun 2023. An guntule hannuwansa biyu, ɗaya daga wuyan hannu, ɗayan kuma daga gwiwar hannun. Wannan ya sa ba zai iya yi wa kansa abubuwa da dama ba, kamar cin abinci ko wanka ko kuma sanya kaya.

Ya ce: “Na san mutumin da ya datse mani hannuwa, amma ba mu taɓa yin ido huɗu ba tun bayan faruwar lamarin''.

Ana zargin Mista Chara da maita ne bayan mutuwar wani yaro, amma ya ce yana sane cewa an kai masa harin ne saboda filin da ya mallaka''.

“Ba na da wata alaƙa da maita. Ina da fili ɗaya, kuma yana a gefen rafi ne, fili ne mai girma sosai.''

An binciki ƴan'uwan Mista Chara da dama a game da yunƙurin kashe shin, amma babu wanda aka gurfanar a kotu. Mista Wanyama na ci gaba da ƙoƙarin ganin ya bi masa haƙƙinsa a kan batun.

Ya ce: “Mutanen da aka taɓa gurfanarwa a kan zargin kisan tsofaffi ba su da yawa. Kuma ina ganin shi ya sa har mutanen da aka samu da kisan kai ba su ganin cewa za a iya yi masu wani abu''.

Bayan shafe watanni yana bincike, shafin binciken ƙwaƙwaf na BBC Africa Eye ya samu damar gano wani da ya aikata irin wannan laifi a baya, wanda ya yi iƙirarin cewa ya kashe mutane aƙalla 20. Ya ce mafi ƙarancin kuɗin da ake biyan sa a duk lokacin da ya aikata kisan shi ne 50,000 na shilings ɗin Kenya, daidai da dalar Amurka 400 (Yuro 310).

Ya sahaida wa BBC Africa Eye cewa: ''Ka sani cewa duk tsohon da aka kashe to ƴan uwansa ne suka bayar da kwangilar kashe shi,''

Da kuma aka tambaye shi a kan ko yana ganin ya dace a kashe mutum, sai ya ce: “Ana iya ganin cewa na aikata wani abu da ba shi da kyau saboda a zahiri ni ne na aikata kisan, amma a bisa doka da kuma a wajen Allah, mutumin da ya tura ni ne mai laifi''.

Hukumar kare haƙƙin ɗan'adam ta Kenya ta gabatar wa Majalisar Dinkin Duniya wani rahoto a cikin watan Fabarairun 2023, inda ta ce: ''Kisa da ƙona tsofaffi da ake zargi da maita da kuma kai masu hari ya yawaita a yankuna irin su Kisii da ke yammacin Kenya da kuma Kilifi da ke gaɓar teku.''

Ta kuma bayyana cewa yunƙurin matasa na neman mallakar filaye ne ya ruruta wutar kisan tsofaffin. Kuma lamarin yana ƙaruwa ne a lokacin rani da ake fama da matsanancin talauci.

Mista Wanyama ya ce lamarin ya zamo wata ''babbar annoba a ƙasar,''

“An fara abin ne daga wani yanki, kuma daga baya ya bazu zuwa kusan ko'ina... Idan ba mu yi wani abu a kai ba babu shakka za a ƙarar da tsofaffinmu.''

A al'adar Afirka, tsofaffi suna da muhimmanci sosai saboda ilimi da baiwarsu.

A Kilifi, lamarin ya ɗauki sabon salo inda tsofaffi ke rina gashin kansu domin kada a gane sun tsufa, da kuma kauce wa yanayin da za a kai masu hari.

Ba kasafai mutum ke tsallake kisa ba a wannan yankin, idan aka zarge shi da maita.

Yanzu dai Mista Chara yana zaune ƙalau babu fargaba, a cibiyar kula da tsofaffi, amma ga mutane irin su Mista Jefwa, har yanzu suna fargabar cewa ko ma waye ya yi yunƙurin kashe shi zai iya dawowa.