Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Halin da tsohuwa ƴar shekara 70 ta shiga a lokacin goyon cikin tagwaye
- Marubuci, Daga Danai Nesta Kupemba
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- An wallafa
Wata dattijuwa mai shekara 70 ta haifi tagwaye bayan da aka yi mata dashen kwan - da aka ƙyanƙyashe - a mahaifarta a wani asibitin Uganda.
Safina Namukwaya ta haifi tagwayen ne - namiji da mace - bayan da aka yi mata tiyata a asibitin haihuwa da ke birnin Kampala.
Ms Namukwaya - wadda ta kasance ɗaya daga cikin matan da suka haihu a shekarunsu na tsufa - ta shaida wa kafar yaɗa labaran ƙasar cewa wannan al'amari abin ''al'ajabi'' ne.
Hukumar asibitin ya taya ta murna, tana mai cewa lamarin ya zarta nasarar bangaren lafiya; ya ma zama nasarar ƙarfi da juriyar da ta nuna a matsayinta na bil-adama''.
Dakta Edward Tamale Sali, ƙwararren likitan haihuwa ne a cibiyar kula da masu juna-biyu ta duniya, ya kuma shaida wa BBC cewa matar ta yi amfani da ƙwan da wata mata da ta ba ta gudunmowa da kuma maniyyin abokin zamanta wajen yi mata aikin kyankyasar tare da dasa mata shi a mahaifarta.
An haifi jariran bayan mako 31 a matayin bakwaini, inda aka sanya su cikin kwalabe a asibitin, domin ci gaba da ba su kulawa, inda kuma Dakta Sali ya ce suna cikin yanayi mai kyau.
"Mun cimma gagarumar nasara - haihuwar tagwaye ga matar da ta fi tsufa a Afirka, shekara 70!'' kamar yadda hukumar asibitin ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Misis Namukwaya ta shaida wa Jaridar Daily Monitor cewa ta sha wahala a lokacin goyon cikin bayan da abokin zaman nata ya yi watsi da ita a lokacin da ya fahimci tawaye za ta haifa.
"Maza ba sa son mace ta faɗa cewa tana ɗauke da cikin ɗa fiye da ɗaya . Tun da aka kawo ni asibitin, abokin zaman nawa bai zo ba'', in ji ta.
Wannan shi ne karo na biyu da Misis Namukwaya ke haihuwa a cikin shekara uku . A shekarar 2020 ma ta haifi 'ya mace.
Ta ce ta fara son haihuwa ne bayan da aka yi mata gori da cewa ita juya ce.
"Idan na ga yadda sauran mata ke yi da 'ya'yayensu abin na ba ni sha'awa, nakan shiga damuwa idan na tuna cewa ba ni da mai kula da ni idan na manyanta''.
Mafi yawan mata kan daina jinin al'ada tsakanin shekara 45 zuwa 55.
A waɗannan shekarun ne kuma mace kan daina fitar da kwai, to sai dai ci gaban kimmiyya ya zo musu da damar samun haihuwa.
Hanyar dashen ƙyanƙyasasshen kwai cikin mahaifar mata da aka fi sani da 'IVF' a turance, na ɗaya daga cikin dabarun da ci gaban zamani ya zo da su.
Akan cire kwai daga mahaifar mace sannan a ƙyanƙyashe shi da maniyyin namiji a dakin ɗakin gwaji.
Daga nan sai a mayar da ƙyanƙyasasshen kwan da ake kira 'ɗan tayi' cikin mahaifar mace domin ci gaba da girma da rayuwa a cikin mahaifar, har ya zuwa lokacin haihuwa.
Indiyawa biyu ƴan shekara 70 sun taɓa haihuwa
A shekarar 2019 ma, wata Ba'indiya mai shekara 73 ta haifi tagwaye bayan yi mata dashen kwai a mahaifa.
Mangayamma Yaramati ta ce ita da mijinta, wanda a lokacin shekararsa 82, sun daɗe suna sha'awar haihuwa, amma matar ba ta taɓa samun ko da ɓatan wata ba, sai a 2019.
Mijinta Sitarama Rajarao ya shaida wa BBC cewa ''Muna cikin farin ciki da murna da samun haihuwar tagwayen.
Samun haihuwar ya kasance muhimmin abu ga ma'auran da suka manyantan, waɗanda suka daɗe suna fuskantar tsangwama a ƙauyensu saboda rashin haihuwa.
"Mutanen ƙauyenmu kan kirani da juya," in ji Misis Yaramati.
"Mun yi ta neman maganin haihuwa, mun je asibitoci masu yawa, kafin Allah ya tarfa wa garinmu nono''.
An haifi jariran ne ta hanyar tiyata, wanda mafi yawanci ita ce hanyar da matan da suka manyanta ke haihuwa.
A 2016 ma wata Ba'indiya ta haifi jariri a lokacin da take shekaru 70 lardin Daljinder Kaur.