Kofin Duniya: Faransa ta zama ƙasa ta farko da ta je zagaye na biyu

An wallafa

Tawagar ƙwallon ƙafa ta Faransa mai riƙe da Kofin Duniya ta zama ta farko da ta samu nasarar zuwa zagaye na gaba a gasar bayan ta lallasa Denmark 2-1.

Tun a jiya Juma'a Qatar mai masaukin baƙi ta zama ƙasa ta farko da aka yi waje da ita daga gasar.

Kylian Mbappe ne ya ci wa Faransa ƙwallayen, inda mai tsaron bayan Denmark Andreas Christensen ya ci wa ƙasarsa ɗaya.

Hakan ya sa Faransa na mataki na ɗaya a Rukunin D da maki biyu. Australiya na da mataki na biyu da maki uku, sai kuma Denmark da Tunisiya masu 1-1.

Kazalika, a ranar Asabar an yi gumurzu tsakanin Saudiyya da Poland inda Poland ɗin ta doke Saudiyya 2-0.

Haka kuma an fafata tsakanin Australiya da Tunisiya a wasan da Australiyar ta yi nasara da 1-0 .