Yaya mamayen ƙasa na sojojin Isra'ila zai kasance a Gaza?

Israel tank
Bayanan hoto, Isra'ila na ta tara dakaru da kayan yaƙi a kusa da Zirin Gaza
    • Marubuci, Daga Jonathan Beale
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakilin BBC kan sha'anin tsaro
  • An wallafa

Isra'ila ga alama tana shirin ƙaddamar da wani mamayen ƙasa a Gaza.

Sojojinta sun yi ta faɗa wa mutane miliyan ɗaya da dubu ɗari ɗaya a arewacin zirin su koma kudu a cikin sa'a 24. A lokaci guda kuma ta yi ta tattara dubun dabatar dakaru da tankokin yaƙi da bindigogin atilare a gaɓar kan iyaka.

Sai dai tura dakarun mamaya ta ƙasa cikin Gaza mai yankunan birnin da ke cunkushe da jama'a, wani aikin soji ne mai cike da hatsari a kusa.

Babu bayani a fayyace game da girman mamayen ƙasa da Isra'ila ke da yiwuwar ƙaddamarwa har yanzu - yaya zurfi da wannan mamaye zai kasance kuma tsawon wanne lokaci za a kwashe ana yi?

Yaushe zai iya faruwa?

An fara duk wani atisayen da ya zama dole wajen gudanar da wannan farmaki na ƙasa.

Manjo Janar Amos Gilead, wani gogaggen soja a rundunar dakarun tsaron Isra’ila (IDF) kuma wanda ya taɓa zuwa cikin Gaza don gudanar da hare-haren soji a baya, ya ce aikin farko da ke gaban Isra’ila shi ne ta kafa gwamnatin haɗin kan ƙasa don samun goyon bayan jama’a kan abubuwan da za su far a gaba.

Ziyarce-ziyarcen diflomasiyya na manyan jami’an Amurka da ‘yan siyasar Turai a baya-bayan nan, sun bai wa Isra’ila damar bunƙasa samun goyon bayan ƙasashen duniya.

Ko da yake irin wannan goyon baya zai iya raguwa idan wannan yaƙi ya ɗauki lokaci, sannan kuma yawan fararen hula da ake kashewa ya yi matuƙar ƙaruwa.

Mutuwar sojojin Isra’ila masu gagarumin yawa a duk wani farmaki da za ta kai, shi ma zai iya gwada tsananin juriyarta.

Ga shirye-shiryen farmakin sojoji, tuni Isra’ila ta tattara dakarunta a kusa da kan iyaka da Gaza. Ta fito da wasu sojojin wucin gadi kimanin 300,000, tare da dakarun dindindin su sama da 160,000.

Saudi troops

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Sojojin Isra'ila na sintiri a yankin da aka kai hari, inda aka kashe fiye da mutum 260 a bikin kaɗe-kaɗe
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Mun zanta da wasu sojojin wucin gadi da iso a baya-bayan nan zuwa kudanci – tsiminsu ga alama a tashe yake, kuma a shirye suke su shiga yaƙi.

Nissim yana ƙasar Sri Lanka lokacin da ya fara jin labarin harin da Hamas ta kai, amma ya biyo jirgin sama na farko da ya taso zuwa Isra’ila don shiga cikin rundunarsa. "Wannan gidanmu ne. Ko da za mu yi faɗa, sai mun kare shi," ya ce.

Shuki ya baro aikinsa na jami’in ciniki ba tare da wani ɓata lokaci ba. "Muna son zaman lafiya," ya faɗa mini. "Amma abin takaici, ya kasa samuwa. Muna shan iskar rayuwa, to amma akwai buƙatar sai mun yi yaƙi don tabbatar da ‘yancinmu na rayuwa."

Israel ga alama ta samu haɗin kai don ɗaukar mataki, lokaci kuma yana tafiya a yayin da suke jiran umarninsu na tafiya yaƙi. Dakaru suna ƙara zaman jira, abubuwa na daɗa zame musu masu wahala su iya ɗorewa cikin ɗamara da zafin tsiminsu.

Gargaɗin Isra’ila ga Falasɗinawan da ke zaune a Gaza cewa su gudu zuwa kudu, wata manuniya ce cewa mataki na gaba na farmakin sojojinta ya kawo jiki.

Shirye-shiryen kai farmaki

Babban aikin Isra’ila na farko shi ne ta tabbatar da tsaron iyakokinta kuma ta kashe ko ta kama tare da titsiye mayaƙan Hamas da suka tsallako kan iyaka kuma suka kashe mutane sama da 1,300 sannan suka sace aƙalla mutum 150.

Tuni dai Isra’ila take ta gudanar da matsanancin hare-hare ta sama inda take far wa manyan sojojin Hamas da cibiyoyin aikinta.

A sama da kwana shida rundunar sojin samanta ta jefa bama-bamai sama da 6,000 a kan Gaza. Idan aka kwatanta, dakarun ƙawance na Nato sun saki bam 7,700 a ɗaukacin yaƙin Libya na 2011.

Mutane sama da 1,500 ne aka kashe a Gaza zuwa yanzu.

Shirye-shiryen mamayen ƙasan kansa, batu na tsananin sirri, sai dai Isra’ila ta yi ta shiryawa wannan lamari tsawon shekaru. Tana horas da dakarunta a wata cibiyar miliyoyin daloli barkaai ta koyon dabarun yaƙi a kan cikin birni a kudancin ƙasar. Ana dai yi wa cibiyar laƙabi da ƙaramar Gaza

Yaƙin cikin gari da na hanyoyin ƙarƙashin ƙasa

A can, sun koyi yadda za su yi faɗa a lungunan da ke tsuke da cunkoson gine-gine da hanyoyin ƙarƙashin ƙasa, waɗanda aka yi imani Hamas ta gina sama da 1,000.

Yaakov Katz, wani tsohon editan jaridar Jerusalem Post kuma mawallafin littattafai masu yawa kan sojojin Isra’ila, ya ce an sauya wa rundunar sojin alƙibla saboda wannan manufa ta ƙwararrun rundunoni – wadda ta ƙunshi injiniyoyi da ke da motocin katafila masu sulke, suna aiki hannu ɗaya da tankokin yaƙi da kuma sojojin ƙasa.

Makomar mutanen Isra’ila da ake garkuwa da su, ta sanya duk wani farmakin ƙasa da za a kai zai iya zama mai sarƙaƙiya.

Makomar mutanen da aka yi garkuwa da su

Manjo Janar Gilead yana cikin waɗanda suka gudanar da tattaunawar da daga bisani ta kai ga sakin wani sojan Isra’ila, Gilad Shalit, wanda Hamas ta riƙe shi tsawon shekara biyar daga shekara ta 2006 zuwa 2011. Daga bisani, an yi musayar sa da fursunoni Falasɗinawa fiye da 1,000.

Hamas

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Burin da Isra'ila ta bayyana shi ne na wargaza Hamas

Manjo Janar Gilead ya ce yayin da sojoji ke da buƙatar su yi la’akari game da makomarsu, “idan ba mu yi wani abu ƙwaƙƙwara ba, muna iya samun kanmu a cikin ƙarin manyan matsaloli".

Sai dai Manjo Janar Amidror ya ce mutanen da ake garkuwa da su ba za su hana ɗaukar kowanne irin mataki ba. "Za mu yaƙi Hamas har sai mun ga ƙarshenta kuma za mu gano waɗanda aka yi garkuwa da su a yayin wannan aiki."

Mene ne burin Isra'ila?

Burin da Isra’ila ta bayyana shi ne wargaza Hamas.

Manjo Janar Gilead, wanda ya shafe kimanin shekara 30 a rundunar tsaron Isra’ila, ya ce hakan ya zarce hare-haren da sojojin Isra’ila suka yi a Gaza shekarun baya wanda "akasari a kan rage ƙarfin" ƙungiyar ne.

A wannan lokacin a cewarsa "muna buƙatar yin wani abu da zai ƙara fita-zakka". Matakin soja da zai haifar da wani ƙwaƙƙwaran sakamako ya yi imani zai zama izina ga sauran abokan gabar Isra’ila a yankin Gabas ta Tsakiya – kamar Hezbollah da ƙasar Iran.

Mista Katz kuwa ya yi imani burin Isra’ila zai kasance ne wajen ganin ta yi abin da zai iya yiwuwa – ta tabbatar cewa Hamas ba ta sake samun ƙarfin soji da za ta iya sake kai farmaki Isra’ila ba. Ya ce Isra’ila "ba za ta so ta sake mamaye Gaza ba, inda za ta ɗauki nauyin kula da mutum miliyan biyu masu gaba da ita".

Sai dai tarihi na baya-bayan nan ya nuna mamayen soji bai cika tafiya kamar yadda aka tsara ba.

Hatta dakarun sojoji mafi ci gaba a duniya ba da wata jimawa ba suna kakarewa – dubi abin da ya faru ga Amurka a Iraƙi da Afghanistan, da kuma baya-bayan nan Rasha a ƙasar Ukraine.

Mamayen sojoji a Gaza wanda ke da tsawon kilomita 40 kawai, ba a maganar girma ba ne, amma sakamakon har yanzu ba a kai ga iya fayyace shi ba, a cewar Laftanal Janar Sir Tom Beckett na Cibiyar Nazarin Dabarun Aikin Soja.

"Maganar gaskiya, babu wani kyakkyawan zaɓi ga mamayen ƙasa ga sojojin Isra’ila a Gaza. Duk irin nasarar da aikin mamayen ya kasance wajen murƙushe Hamas a matsayinta na ƙungiya mai gwagwarmaya da makamai, fa’idar harkokin siyasar Hamas da goyon bayan jama’a ga nuna bijirewarta za su ci gaba.

"Ko da Isra’ila ta sake mamaye Gaza don ta karɓi iko da ita ko kuma, ta janye bayan farmakin, sallama yanki ga mutanen da bijirewarsu ita ce rayuwa."