Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Za a kara tsakanin Benzema da Lewandowski a El Clasico
Real Madrid za ta karbi bakuncin Barcelona a wasan mako na tara a gasar La Liga da za su kara ranar Lahadi a Santiago Bernabeu.
Wannan shi ne wasan farko da za su yi a wasan na hamayya da ake kira El Clasico a babbar gasar tamaula ta Sifaniya a bana.
Barcelona ce ta daya a kan teburi mai maki 22, iri daya da na Real Madrid, wadda take ta biyu mai rike da kofin bara.
Karawar ta hamayya za a yi ne tsakanin Karim Benzema da Robert Lewandowski, wadanda suka yi suna wajen cin kwallaye.
Benzema ya buga wasa biyar a bana a La Liga ya ci kwallo uku, shi kuwa Lewandowski mai wasa bakwai yana da kwallo tara a gasar La Liga ta bana.
Lewandowski ya koma Barcelona a bana daga Bayern Munich.
Wasan da suka buga a kakar 2021/22
2021/2022
Spanish La Liga Lahadi 20 ga watan Maris 2022
- Real Madrid 0 - 4 Barcelona
Spanish Super Cup Laraba 12 ga watan Janairun 2022
- Barcelona 2 - 3 Real Madrid
Spanish La Liga Lahadi 24 ga watan Oktoban 2021
- Barcelona 1 - 2 Real Madrid
'Yan wasan Real Madrid:
Masu tsaron raga: Lunin, Luis López, Cañizares.
Masu tsaron baya: Carvajal, E. Militão, Alaba, Vallejo, Nacho, Odriozola, Lucas V., Rüdiger, F. Mendy.
Masu buga tsakiya: Kroos, Modrić, Camavinga, Valverde, Tchouameni.
Masu cin kwallaye: Hazard, Benzema, Asensio, Vini Jr., Rodrygo, Mariano
'Yan wasan Barcelona:
Ter Stegen, Piqué, Sergio, O. Dembélé, Pedri, Lewandowski, Ansu Fati, Ferran, Marcos A., Jordi Alba da kuma Kessie.
Sauran sun hada da S. Roberto, F. De Jong , Raphinha, Kounde, Eric, Iñaki Peña, Balde, Gavi, Pablo Torre da kuma Arnau Tenas.
Haka kuma dan wasan Faransa, mai tsaron baya Jules Kounde ya murmure zai iya buga wasan na hamayya.