Juyin Mulkin Nijar: Jarrabawa ga dimokraɗiyyar Afirka ta Yamma

    • Marubuci, Yusuf Akinpelu
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Lagos
  • An wallafa

Bola Ahmed Tinubu - wanda shi ke riƙe da ragamar mulkin Najeriya, ƙasar da ta fi kowace ƙasa a yankin yammacin Afirka ƙarfin faɗa a ji- na kallon juyin mulkin da a ka yi a Nijar, a matsayin jarrabawar makomar dimokraɗiyyar Afirka ta Yamma.

A matsayinsa na shugaban ƙungiyar ƙasashen yammacin Afrika, yana fuskantar gagarumin ƙalubale sakamakon juyin mulkin da sojoji sukayi a Nijar, yayin da yawancin ƙasashen yammacin Afirkan ke fama da yaƙi da masu iƙirarin jihadi.

Shugaba Tinubu ya nuna damuwarsa kan juyin mulkin da aka yi a ƙasashen Burkina Faso da Mali da kuma Guinea a lokacin da ya ƙarɓi ragamar jagorancin shugabancin Najeriya a watan Mayu.

Yana mai cewa akwai buƙatar ƙungiyar Ecowas ta ƙara ƙaimi wajen kawo ƙarshen juyin mulki a yankin da kuma yaƙar masu ta da ƙayar-baya da yankin ke fama da su.

Bayan da shugaban dakarun da ke tsaron fadar shugaban Nijar ya hamɓarar da gwamnatin Mohammed Bazoum, Tinubu ya yi martani kan hakan, inda ya kira taron gaggawa na shugabannin ƙasashen yammacin Afrika a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja a ranar lahadin da ta gabata.

Ƙungiyar Ecowas ta amince da ƙaƙaba wasu takunkumai ga ƙasar ta Nijar, waɗanda suka haɗa da, katse layin wutar lantarkin Yamai baban birnin ƙasar da wasu manyan biranen ƙasar da Najeriya ta yi kamar yadda hukumar samar da wutar lantarkin Nijar ta sanar.

Ecowas ta kuma bai wa sojojin Nijar wa'adin mayar da mulkin ƙasar ga hamɓararren shugaban a cikin mako guda, ko ta ɗauki "dukkan matakan da suka dace ciki har da amfani da ƙarfin soji.

Manyan hafsoshin ƙasashen yammacin Afirka sun yi taro a Abuja babban birnin Najeriya.

'Juyin mulki cin fuska ne ga aƙidar Tinubu'

Tinubu ya taka rawar gani wajen yaƙi da mulkin soji a Najeriya a shekarun 1980.

"Ina ganin kamar yana kallon wannan juyin mulkin na Nijar a matsayin cin fuska ga aƙidarsa ta tabbatar da dimokraɗiyya, musamman da ya ke shugaban ƙungiyar Ecowas," inji Wole Ojewale, wani mai sharhi a cibiyar da ke nazari kan harkokin tsaro a Najeriya.

Abu mafi mahimmaci shi ne, juyin mulkin na da alaƙa kai-tsaye da Najeriya.

Ƙasashen biyu na da iyakar da ta kai sama da kilomita 1,500, kuma suna da ƙwaƙƙwarar dangantaka ta ɓangaren al'adu da kasuwanci tun lokacin mulkin mallaka da kowanensu ke ƙarkashin daular Usumaniyya.

Tsaron ƙasashen biyu a haɗe yake saboda ƙungiyar Boko Haram na gabatar da ayyukanta a ɓangarorin ƙasashen biyu, yayin da ƙasashen suka yi haɗin gwiwar soji daga Najeriya da Nijar da Chadi da kuma Kamaru da suke yaƙi da 'yan ta'addan.

Dakarun tsaron na samun goyon bayan sojin Amurka da Birtaniya da kuma Faransa , daga bisani kuma suka samar da sansanoni biyu a Nijar.

A shekarar 2022, Nijar ta samar da kashi 4 na makamashin Uranium a duniya, kuma ita ce ƙasar da ta fi kowace ƙasa samar da makamashin a Afrika.

Ecowas da ƙawayenta na ƙasashen yamma ba za su so makamashin Uranium ɗin da ke ɗauke da tiriri mai guba ya faɗa hannun maƙiya ba, musamman a yankin da masu iƙirarin jihadi da Rasha ke gudanar da ayyuka.

Bayan juyin mulkin, ƙasashen Mali da Burkina Faso, ƙasashen biyu sun mayar da akalarsu ga Rasha, hakan ne ya sa sojojin da ke mulkin Nijar ke ƙoƙarin karkata ga Rasha.

Shugaban Chadi Mahamat Idriss Déby , wanda sojojin ƙasar suka ɗora bisa mulki bayan an kashe mahaifinsa a shekarar 2021, ya je Nijar a ranar Lahadi domin jan hankalin shugaban sojojin su girmama buƙatar Ecowas.

Chadi ba ta cikin ƙungiyar Ecowas, to amma duk da haka Mr Deby ya halarci taron ƙungiyar na ranar lahadi.

A matsayinsa na jarumi kuma gawurtaccen soja, Ecowas ta ga ya dace ta wakilta shi domin ya tattauna da sojojin na Nijar, tare da roƙon su da su janye.

Sai dai sojojin ba su amince da buƙatar ta Ecowas ba.

Sojojin sun fito ƙarara domin nuna adawarsu da ƙasashen Yamma da kuma Ecowas, yayin da dubban magoya bayansu suka fito bisa manyan titunan Yamai a ranar Lahadi suka nuna goyon bayan su ga sojojin ta hanyar gudanar da zanga-zanga, inda suka kai hari ga ofishin jakadancin Faransa, tare da ɗaga tutar ƙasar Rasha.

Hakan ba zai zama wani ma'auni da za a iya gane ko sojojin na da rinjayen magoya baya a ƙasar, ko akasin haka ba.

Saboda a shekarar 2022, wani bincike ya nuna yadda fiye da rabin ƴan ƙasar suka amince da salon mulkin ɗimokraɗiyar.

Kaso biyu cikin uku na binciken yana cewa sojoji na yin juyin mulki ne a lokacin da suke ganin shugabannin da aka zaɓa sun gaza.

Wannan shi ne batun da masu juyin mulki da magoya bayansu ke amfani da shi wajen kare kansu a duk lokacin da irin haka ta faru.

Sojoji masu mulki a Nijar da Burkina Faso da Mali sun gargaɗi Ecowas kan tura sojoji Nijar, suna masu cewa yin hakan daidai yake da "ƙaddamar da yaƙi" kuma za su shigar wa sojojin Nijar faɗa.

Ana hasashen shigar da sojoji zuwa Nijar zai iya haifar da rikici a ƙasar.

Ƙungiyar Ecowas ta aika da dakarunta wasu ƙasashen da suka haɗa da Laberiya da Saliyo da Guinea-Bissau da kuma Gambiya domin samar da zaman lafiya.

Wannan shiga tsakanin da Ecowas ke yi ta hanyar tura dakaru, wani ɓangare ne na sauke nauyin da yake wuyanta na "tabbatar da zaman lafiya a yankin", koda yake ana zargin dakarun ta da take haƙokin bil adam.

Mr Ojewale ya ce baya da tabbacin ko ƙungiyar Ecowas na da ƙarfin sojin da za ta iya aikawa Nijar, musamman idan aka yi la'akari da yadda wasu daga cikin ƙasashen ke fama da matsalar tsaro.

"Ƴan albarkatun ƙasa ƙalilan da suke da su na iya ƙanƙancewa,"

Masu sharhi sun yi imanin cewa rikici tsakanin ɓangarorin biyu "lamari ne wanda dole ɓangare guda ya yi nasara wani kuma ya faɗi", kuma zai iya ta'azzara ayyukan jin ƙai a yankin.

"Lamarin zai iya jikkata mutane saboda wasu za su yi ƙoƙarin shiga inda ake yaƙin, saboda haka sasantawa cikin sauƙi shi ne abin da yafi," inji shi.

Akwai kuma tambayar da ake yawan yi game da halin da hamɓarren shugaban yake ciki da sojojin ke ci gaba da tsarewa.

Wani mai sharhi, Jaafar Abubakar, ya ce akwai yiyuwar ya zama makamin da sojojin za su yi amfani da shi wajen sasanci tsakanin su da Ecowas.

"Abin da ya fi kyau shi ne sojojin su tabbatar sun kiyaye lafiyar Bazoum, saboda idan suka kashe shi, za a kalle su a matsayin ƴan tawaye marasa madogara."