Daga Bakin Mai Ita tare da Nadiya ta Manyan Mata

Daga Bakin Mai Ita tare da Nadiya ta Manyan Mata
An wallafa

Filin Daga Bakin Mai Ita na wannan makon ya tattauna da Rabiatu Kurfi, wadda aka sani da Nadiya a fim ɗin Manyan Mata.

Tauraruwar fina-finan haifaffiyar birnin Abuja ce duk da cewa 'yan asalin garin Dutsinma ne a jihar Katsina.

Bayan fim ɗin Manyan Mata, tana kuma cikin fim ɗin Kwana Casa'in na tashar Arewa 24.