Labari mai daɗi na gano Hanifa, yarinyar da ta ɓace a Kano tsawon kwanaki

An wallafa

Bayan ta dawo daga makarantar Islamiyya da misalin karfe 5 na yamma a ranar Asabar, sai aka yi mata wanka sannan sai ta fita waje don yin wasa tare da sauran yara.

Wannan shi ne lokaci na karshe da aka ganta a ranar.

Khalifa Hudu, kawun Hanifa Usama, ƴar kimanin shekaru hudu da haihuwa, ya shaida wa BBC Pidgin cewa bayan ya samu labarin cewa 'yar dan uwansa wadda ta je ta zauna da su na wani wani tsawon kwanaki tare da kakarta a unguwar Gobirawa da ke jihar Kano ta ɓata, sai hankalinsa ya tashi.

Ya ce, "Bayan sa'a guda suna wasa kowanne yaro ya koma gida sai aka ji Hanifa shiru ba ta shigo gida ba, sai ni da sauran mutane muka fita don ganin me ke faruwa."

Khalifa ya ce, bayan sun duba gidajen ƙawayen Hanifa ba su ganta ba daga nan ne sai suka fara fargaba da kuma shiga cikin tashin hankali.

Ya ce, "Abu na gaba da muka yi shi ne sai muka garzaya zuwa ofishin 'yan sanda da na Hisba don kai rahoto a kan ɓatan Hanifa, a lokacin abin da muke tunani shi ne ka da abin da ya faru da wata Hanifar a baya ya faru da tamu Hanifar."

Mahaifiyar Hanifa, Hauwa Hamidan Ibrahim, ta shaida wa BBC Pidgin cewa, Hanifa ta je gidan kakarta da kawunta ne don ta yi ɗan hutu.

Ta ce, " A lokacin da suka kira ni ranar Asabar da yamma suka ce ba su ga Hanifa ba, sai hankalina ya tashi na tabbata da an auna jinina na san ya hau, saboda babu abin da ya dawo mini illa abin da ya faru da wata Hanifa a baya a Kano."

Mahaifiyar Hanifar ta ce, "Daga nan na shiga cikin damuwa na kasa zaune na kasa tsaye, sai kawai na tafi ofishin Hisba na kai rahoto, anan ne suka tambaye ni sunan 'yata na fada musu cewa sunanta Hanifa, a nan ne suka ce, 'to fa, wata Hanifar ta sake ɓata ke nan?

Tun daga wannan rana babu abin da nake illa kuka musamman idan na tuna da abin da ya faru da mai irin sunanta, sai na ji hankalina ya kara tashi."

Yadda aka ga Hanifa

Mahaifiyar Hanifa ta ce tun daga ranar Asabar din ita da sauran 'yan uwa da abokan arziki suka rinka yawo waje-waje suna neman Hanifa.

Ta ce sai a ranar Litinin kwatsam sai ga labari mai dadi, wanda ta ce shi ne labari mafi dadi da ta taɓa ji a rayuwarta.

Mahaifiyar Hanifa ta ce, "Ina zaune a ranar Litinin da rana, sai kawai na ga ana kirana a waya da wata lamba, aka tambaye ni ke ce Mamar Hanifa? To mun ga 'yarki."

"Ba zan taba mantawa da wannan rana ba a rayuwata" in ji ta.

Ta ce mutumin da ya kira ta ya ce mata a Rijiyar Lemo yake, don haka mu je can an ga Hanifa tana gidan mai unguwa.

"Daga baya ne bayan mun je muka gano cewa wata mata ce ta ga Hanifa ita kadai tana gararanba sai ta dauketa ta kai ta gidanta ta zauna tare da ita da 'ya'yanta kafin daga bisani ta kai rahoto gidan mai unguwar yankin."

Mamar Hanifa ta ce ta so a ce abin da ya faru da waccar Hanifar da mai makarantarsu ya yi garkuwa da ita ya kuma kasheta daga baya, ya faru da tata Hanifar.

Ta ce," Tun daga nan bayan ta ga 'yarta, duk inda take tana tare da ita, ba na barinta zuwa ko fita, ko ina tana katarata don ba na son jin wani labari kuma."

Dangane da batun ko za ta sake barin ta ta je gidan kakarta da kawunta inda abin ya faru, ta ce ko shakka babu za ta je, kuma abin da ya faru da Hanifa zai sa kowa ya shiga taitayinsa a rinka sa ido sosai a kan zirga-zirgar yara.

Mahaifiyar ta ce yarinyar 'yar shekara hudu tana da yayye uku, kuma za ta fara zuwa makaranta idan suka koma Legas da zama inda mahaifinta yake aiki.

Labarin Hanifa wanda ya gigita Kano da ma Najeriya

A watan Yulin shekarar 2022 ne, babbar kotu a Kano ta yake wa Abdulmalik Tanko, mai makarantar Noble Kids Academy, hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda samunsa da laifin kashe Hanifa Abubakar 'yar shekara biyar wadda kuma daliba ce a makarantar tasa.

Mai Shari'a Suleiman Na Abba, ya kuma yanke wa Hashim Isyaku wanda ya taimaka aka binne gawar Hanifa hukuncin kisa ta hanyar rataya shi ma.

Yayin da ita kuma Fatima Musa, aka yanke mata hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekara daya saboda rawar da ta taka wajen ajiye Hanifa a wajenta.

Kisan Hanifa Abubukar, ya girgiza Kano da ma Najeriya baki daya inda aka rinka yada labarin a kafafan sada zumunta.

Mutane da dama sun yi alawadai da kisan da aka yi wa yarinyar ciki har da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.