Wace riba Najeriya za ta samu a ƙungiyar Brics?
- Marubuci, Isiyaku Muhammed
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 3
A ranar Juma'a ne bayanai daga ma'ikatar harkokin Najeriya suka bayyana cewa Najeriya ta bi sahun ƙasashen duniya da suka shiga ƙungiyar tattalin arziƙi ta Brics a matsayin mambar da aka girmama.
Taron ƙasashe waɗanda tattalin arzikinsu ke bunƙasa na bana wato Brics, wanda aka yi daga ranar 22 zuwa 24 ga Oktoba a Rasha ne aka fara muhawara a kan riba ko akasin shiga ƙungiyar.
Taron na bana, wanda ya samu halartar shugaban majalisar ɗinkin duniya, Antonio Guterres, ya zo da sabon sauyi, inda sababbin mambobin ƙungiyar, waɗanda suke da tattalin arziki mai girma irin su China da Turkiyya da Saudiyya suka halarta.
Rahotanni sun nuna cewa Rasha ta shige gaba wajen ɗaukar nauyin taron ne domin nuna wa ƙasashen yamma ƙwanji.
Yanzu dai ƙasashen Afirka guda uku ne kawai suke ƙungiyar: Afirka ta Kudu da Egypt da Ethiopia.
Ga ƙananan ƙasashe waɗanda tattalin arzikinu ke bunƙasa, ana gani shiga ƙungiyar Brics za ta ba su wata dama domin haɓaka tattalin arzikinsu, da shiga alaƙar kasuwanci da samun bashi mai sauƙi daga manyan ƙasashen duniya.
Shigar ƙasashen na Afirka uku ƙungiyar ta sa aka fara tunani tare da hasashen ribar da Afirkar baki ɗaya za ta samu daga ƙungiyar.
Sai dai kasancewar a Afirkar, ana ganin Najeriya a matsayin ƙasa da ke matuƙar muhimmanci, musamman a ɓangaren tattalin arziki, sai labarin za ta shiga ƙungiyar ya faranta ran wasu.
Sai dai kasancewar kowace ƙasa da take shiga ƙungiyar, da ma kowace haɗaƙar ƙasashe tana da muradun da take da burin samu, wannan ya sa ake muhawara a kan wane amfani Najeriya za ta samu da shiga ƙungiyar.

Asalin hoton, Getty Images
Wace riba Najeriya za ta samu a Brics?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Game da ko akwai tasiri da Najeriya za ta samu, BBC ta tuntuɓi Farfesa Tukur Abdulƙadir na Jami'ar Jihar Kaduna, inda ya ce wannan babbar dama ce ga Najeriya.
"Akwai fa’ida sosai ta shiga ƙungiyar Brics saboda ƙungiya ce da tasirinta ke ƙara fitowa fili, kuma muhimmancinta yake ƙara ƙarbuwa, musamman a tsakanin ƙasashe masu tasowa saboda akwai tanade-tanade da ƙungiyar ke da shi na tunkurar matsalolin danniya na manya-manyan ƙasashen musamman yammacin Turai da arewacin Amurka da hukumomin kuɗi na duniya irin su bankin duniya da asusun bada lamuni IMF da kuma tasirin dalar Amurka a tattalin arzikin duniya." In ji farfesa Tukur.
Farfesan ya ƙara da cewa, "Na karanta a wata jarida ministan kuɗi na Najeriya yana cewa Najeriya za ta rungumi tsare-tsare rage amfani da dala a tsarin kasuwancinta da tattalin arzikinta," in ji shi, inda ya ƙara da cewa haka ƙasashen duniya suke yi.
"Misali Iran na fuskantar takunkumi na tattalin arziki daga Amurka da wasu ƙawayenta na yammacin turai, amma tana sayar da manta ga ƙasashen irn su China da India, kuma da ƙasashen ƙasarsu suke amfani."
Ya ce Najeriya za ta iya amfani da wannan a matsayin wata dama, "amma sai shugabannin ƙasar sun yi tunani irin haka. Amma dai ya gandanta da yanayin siyasar duniya."
A game da yadda harkokin Najeriya kusan komai ya ta'allaƙa da dala, inda hakan ya sa wasu suke fargabar janyewa daga dalar za ta iya jefa ƙasar cikin damuwa, sai Farfesan ya ce ai wannan ne babban ribar da Najeriya za ta samu.
"Idan shugabanninta suka farka daga ɗimaucewar da suke ciki na rungumar jarin hujja da 100 bisa 100 da kuma yadda suke haba-haba da yammacin turai da hukumomin tattalin arzikin duniya. Ko ƙasashen da aka cewa aka yanke wa jari hujjan cibiya, ba sa amfani da ita 100 bisa 100 wasu suna tallafa wa mutanensu."
A wani ɓangaren kuma, ana ganin ƙungiyar Brics suna adawa da ƙasashen yamma ne, wanda hakan ya sa ake fargabar ko ƙasashen da suke ƙungiyar za su iya fuskantar ƙalubale daga ƙasashen na yamma.
A game da wannan, farfesan ya ce, "Ai Najeriya da a ce akwai shugabanci mai kyau ta fi ƙarfin ta zama ƴar amshin shatar wasu ƙasashe. Ƙasar da ke da sama da mutum miliyan 200 da ɗimbin arziki, kuma duk wani abu da ake buƙata domin ƙasa ta cigaba a zamanin nan na ƙarni 21 tana da shi. Saboda haka shugabanci na gari kawai ta rasa."
"Shugabannin da ake da su ne suka ɗauka ƙasa ba za ta cigaba ba sai ta zama ƴar amshin shata. Wannan shi ne naƙasun Najeriya, ba shiga ƙungiyar ba. Sannan kuma duniya tana buƙatar kishiyoyi na manyan ƙasashe da hukumomin kuɗaɗe saboda haka ne zai taƙaita tasirin waɗanda suka mamaye tattalin arziki kuma suke amfani da kuɗaɗensu a matsayin makami a wannan ƙarni."











