Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ƴan Real Madrid da suka je Mallorca buga La Liga
Real Madrid ta ziyarci Real Mallorca, domin buga wasan makon farko a La Liga ranar Lahadi a filin wasa na Son Moix.
Real Madrid ce mai rike da La Liga da ta lashe a kakar da ta wuce tare da Champions League.
A kakar da ta wuce a babbar gasar gasar tamaula ta Sifaniya, Real Madrid ta doke Mallorca gida da waje 1-0 a karawa biyun da suka yi.
Kakar 2023/2024
Spanish La Liga Asabar 13 ga watan Afirilun 2024
- Mallorca 0 - 1 Real Madrid
Spanish La Liga Laraba 03 ga watan Janairun 2024
- Real Madrid 1 - 0 Mallorca
Real Madrid za ta buga wasan na ranar Lahadi da kwarin gwiwa, bayan da ta lashe Uefa Super Cup a Warsaw a Poland ranar Laraba, inda ta ci Atalanta 2-0.
Tuni kociyan Real Madrid, Carlo Ancelotti ya bayyana waɗanda ya je da su Mallorca, domin buga wasan farko a babbar gasar tamaula ta Sifaniya kakar 2024/25.
Jerin ƴan wasan Real Madrid:
Masu tsaron raga: Courtois, Lunin da kuma Fran.
Masu tsare baya: Carvajal, Militão, Lucas V., Vallejo, Fran García, Rüdiger, F. Mendy ada kuma Jacobo.
Masu buga tsakiya: Bellingham, Valverde, Modrić, Tchouameni, Arda Güler da kuma Ceballos.
Masu cin ƙwallaye: Vini Jr., Mbappé, Rodrygo, Endrick da kuma Brahim.