Gasar cin kofin duniya ta kwallon gora ta 2023: Shin Indiya za ta iya maimaita nasarar da ta samu a 1975?

An wallafa

Karo na karshe da Indiya ta lashe Kofin Duniya na wasan kwallon gora, abubuwa sun bambanta matuka.

Kusan rabin karni ke nan, kuma Indira Gandhi ce Firaminista a lokacin da Indiya ta daga kofin a watan Maris na 1975 a Kuala Lumpur – shekara takwas gabannin nasara ta farko da indiya ta taba samu a rayuwarta ta lashe Kofin Duniya na wasan kurket.

An dade kam da samun wannan nasara tata mai tarihi ba, da za a iya cewa shekara 48 ke nan.

 A matsayinta ta biyar a duniya, Indiya za ta karbi bakuncin gasar wasannin kwallon gora ta cin Kofin Duniya ta karo na biyu a jere. An gudanar da wasanni a biranen Bhubaneswar da Rourketa da ke gabashin jihar Odisha (tsohuwar Orissa)

 

Zuwa yanzun Indiya ta yi wasannin guda biyu – daya ta kara da Spain, wanda suka yi nasara, sai wasa na biyu suka kara da Ingila ranar Lahadi da daddare, da aka tashi babu wanda ya ci wani.

Abin da ya yi saura a yanzun shi ne a matakin karawarsu ta karshe, ko Indiya za ta samu nasara wajen lashe wasansu na kusa da na karshe kai tsaye ko za su bukaci sai sun ci gaba da wasa na gaba.

Bayan wasanni biyu, Indiya da Ingila kowacce tana da maki hudu, inda Ingila take kan gaba da bambancin kwallo guda daya.

Indiya ba ta da wata fargaba sosai da abokan karawarta da ke Wales, da za su fafata a ranar 19 ga watan Janairu. Indiya za ta so ta ga ta samu nasara domin kasancewa ta kawar da bambancin da ke nan, har ta ma matsa gaba (bambancin da ke tsakanin yawan kwallo da aka ci, da yawan kwallon da kungiyar wasa ta yi asararsu) domin samun matsayi kai tsaye a wasannin kusa da na karshe.

Abin da zai sa Indiyawa su dan saki jiki shi ne Ingila tana da wacce za ta kara da ita, da ba kanwar lasa ba ce a wasa na gaba a Spain, wanda zai iya dakile kokarinta na kai wa da nisa a lissafin kwallayen da ake nema.

A takaice dai kungiyoyi na kasashe 16 ne suka karkasu zuwa rukuni guda hudu, inda Indiya ta tsinci kanta a rukunin D tare da Ingila, da Spain da Wales.

Kungiyoyin da suke rukuninsu da suka kara da wasu lokaci guda sun samu tsallakawa zuwa wasanni na kusa da na karshe. Wasannin guda hudu na kusa da na karshe da suka yi saura, za a su wa za su yi nasara a wasannin da za a yi tsakanin wadanda suka kammala na biyu da na uku.

A lissafin na yanzun dai Australia ta 1 a duniya da wacce take tashe a yanzun a zakarun wasannin Olympic Belgium, su ne wadanda aka fi so da ludayinsu yake bisa dawo. 

A cikin sauran bangarorin da suke da karfi a tsarin su ne, wadanda suke tashe a zakarun Turai, Netherlands, da Ingila, da Jamus.

Tabbas ba za a iya cire Indiya a cikin lissafi ba. Bangare ne da ya kai lambar jarunta ta Olympic gida, bayan shekara 41, kuma ta san abu daya zuwa biyu, a game da kawo karshen fari mai tarihi.

Yana da masu tsaron gida masu kyan gaske.

Wannan ya nuna a wasanninta biyu da Indiya ta yi, tana da nasara domin kuwa ba a ci ta ko daya ba.

Abin da ya fi radadi a wasan na Lahadi kodayake shi ne dan wasa na yanzun da ya fi kowanne iya gara kwallo a tsakiyar fili, Hardik Singh, sai da aka taimaka masa aka fitar da shi daga fili sakamakon raunin da ya ji.

Daga bisani mai horar da `yan wasan Reid  ya kawar da fargabar da `yan kallo suka fara, inda ya ce musu “raunin bai yi tsanani kamar yadda aka dauka da farko ba”

Har ila yau Indiya tana buga wasanninta ne a gida, kuma a jihar da a kowanne lokaci take ba da fifiko ga wasannin motsa jiki.

Jihar Odisha ta shiga lamarin a matsayin babbar mai daukar nauyin kungiyar wasannin kwallon gora ta kasa a 2018 a kan kudin Indiya rupe ($18.3m, £15m) na tsawon shekara 5, ta sake daukar nauyinta na karin wasu shekaru 10 a 2021.

Jihar ta karbi bakuncin wasannin guda biyu na cin kofin duniya, ta gina filin wasa mai cin mutum 20,000 tun daga tushe, a Rourkela domin wasannin da ake kan yi a yanzun haka.

Filin wasan na Birsa, mai kujerun zama irin na zamani, ya zama abin da ake ta tattaunawa a kan sa, a soshiyal midiya.

A watan Nuwamba, gwamnatin Odisha ta sa rupee biliyan 10.98 a kasafin kudi na jihar na shekarar 2922-2023 domin gasar cin Kofin Duniya. Za a yi amfani da kudin ne wajen gina filin wasa na Rourkela, don daukaka matsayin filin wasa da ake da shi a Bhubaneswar, da kawata biranen.

Zuwa yanzun dai jama`a suna tan a`am da wasannin. An sayar da tikitin kallon wasannin na Indiya, kuma filayen wasa suna cika makil ranakun da ake wasannin.

 Idisha, musamman kabilunta, ta dade tana samar da jerin `yan wasan kwallon gora. Kungiyar kwallon ta yanzun tana da mutum biyu- Amit Rohidas da Nilam Xess da suka fito daga jihar.

Babban Minista Naveen Patnaik, wanda aka fahimci shi da kansa ya dan taba wasan a lokacin da yake dan makaranta, y sanar da ladar rupi miliyan daya ga `yan wasan a lokacin da aka soma gasar.

Su kuwa `yan kungiyar wasan Indiya ta 1975, da suka hallara a Odisha domin wasannin saboda gayyatar da wadanda suka shirya gasar suka musu, dole kungiyar ta yanzun ta nuna wa duniya cewa, ita ma ba kanwar lasa ba ce.

A lokacinsu Kungiyar Olympic ta Indiya (IOA) da sabuwar Hukumar Kwallon Gora ta Indiya (IHF) da aka zaba sabuwa sun ta musun wa zai dauki nauyin kungiyar, makwanni kafin gasar ta cin Kofin Duniya.

Said a `yan wasan suka roki gwamnatin tarayya  ta sa baki, har suka ma yi barazanar kin halartar gasar ta cin Kofin Duniya gabadaya, in har ba a warware duka takaddamar da ta taso ba.

Gwamnatin ta yi tayin biyan kudaden tafiye-tafiye, a lokacin ne kungiyar karkashin jagorancin Ajitpal Singh, ta hau jirgin sama, ta bar kasar zuwa gasar cin Kofin Suniya.

Wasa na karshe fafatawa ce tsakanin Indiya da Pakistan, inda Ashol Kumar- dan fitaccen dan wasan kwallon gora Dhyan Chad – ya ci kwallon da ta zame musu nasara.

Sai dai, yanzun aka fara wasannin, wanda ya yi wuri, a yi alkawura, sai dai idan aka yi la`akari da wasannin guda biyu na farko da Indiya ta yi, da alama kungiyar ba za ta yi sanya ba, wajen ganin ta yi dukkan kokarin da za ta yi a gida, don kai bantenta.