Arsenal ta raba maki da Palace a Premier League

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Arsenal da Crystal Palace sun tashi 2-2 a wasan mako na 34 a Premier League da suka kara ranar Laraba a Emirates.

A minti na uku da take leda Arsenal ta ci ƙwallo ta hannun Kiwior daga baya Palace ta farke ta hannun Ebere Eze.

Sai dai sauran minti uku su je hutun rabin lokaci ne, Arsenal ta kara na biyu ta hannun Leandro Trossard.

Sauran minti uku a tashi daga fafatawar Palace ta farke ta hannun Jean-Philippe Mateta, hakan ya sa suka raba maki a tsakaninsu.

Arsenal tana mataki na biyu a teburin babbar gasar tamaula ta Ingila da maki 67, bayan kammala wasan mako na 34.

Ranar Lahadi, Liverpool wadda take ta ɗaya a teburi da maki 79, za ta kece raini da Tottenham a wasan mako na 34 a Premier League.

Kenan ƙungiyar Anfield na bukatar koda maki ɗaya a ranar Lahadi daga nan ta lashe kofin Premier League na kakar nan na 20 jimilla.

Bayan wasan Arsenal ta yi da Palace, za ta fafata da Paris St Germain a Champions League a Emirates zagayen daf da karshe ranar Talata 29 ga watan Afirilu.

Arsenal ta kawo wannan matakin a gasar zakarun Turai ta kakar nan, sakamakon fitar da Real Madrid da cin 5-1 gida da waje a daf da na kusa da na karshe.

Ita kuwa PSG, wadda ta ci Manchester City a Champions League a bana ta fitar da Liverpool a zagayen ƴan 16, ita ta yi waje da Aston Villa a kwata fainal.

Daga nan Arsenal za ta karɓi bakuncin Bournemouth a wasan Premier League a Emirates ranar Asabar 3 ga watan Mayun 2025.