Ko nasarar da Ahmed Musa ya bai wa Kano Pillars za ta ɗore?

Asalin hoton, Ahmed Musa/Facebook
Kyaftin ɗin tawagar Super Eagles Ahmed Musa ya ja hankalin masu bibiyar ƙwallon ƙafa a Najeriya, musamman masoya gasar Firimiyar Najeriya da kuma ƙungiyar Kano Pillars ta Kano.
Ɗan wasan ya zura ƙwallo biyu, sannan ya ɓarar da fanareti a wasansa na farko bayan ya dawo ƙungiyar ta Pillars, a wasan da ‘sai masu gida’ ta doke Sunshine Stars da ci biyu da nema a filin wasa na Muhammad Dikko da ke jihar Katsina a ranar Lahadi 6a ga Oktoba.
Wannan shi ne wasa na biyar na gasar Firimiyar Najeriya na kakar 2024/2025.
Ɗan wasan ya zura ƙwallonsa na farko a minti huɗu da fara wasa, sannan ya ƙara jefa ƙwallo na biyu a minti shida bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.
Saura ƙiris Musa ya samu nasarar cin ƙwallo uku rigis a wasan, amma ya yi rashin nasarar, inda ya ɓarar da bugun fanareti a minti na 70 a wasan.
Da yake bayyana farin cikinsa, Ahmed Musa ya rubuta a shafinsa na Facebook cewa, “na yi farin cikin dawowa Kano Pillars. Ina godiya ga dukkan ma’aikatan ƙungiyar da abokan wasana da masu horar da ƴanwasa bisa wannan damar da suka ba ni. Sannan magoya bayannmu da ma duk waɗanda suka zo kallonmu, muna godiya. Zura ƙwallo biyun nan da na yi somin-taɓi ne,” in ji shi.
Wannan shi ne karo na uku da Ahmed Musa ya taka leda a ƙungiyar Kano Pillars.
Ya fara taka tamaula a ƙungiyar ne a kakar shekarar 2009 zuwa 2010, inda ya zura ƙwallo 18 a wasa 25 da ya buga, inda daga Pillars ɗin ya bar ƙasar, ya tafi ƙungiyar VVV Venlo ta ƙasar Netherland.
Ya sake dawowa a shekarar 2021 bayan ya bar ƙungiyar Al Nassr ta Saudiya, inda ya buga wasa 8. Sai kuma wannan kakar da ya dawo, bayan ya bar ƙungiyar Sivasspor ta Turkiyya a shekarar 2024.
Yanzu dai abin jira a gani shi ne ko fara wasan da ƙafar dama zai ta ɗore bisa la'akari da yadda a baya ya koma ƙungiyar kuma ya buga mata wasanni 8 ba tare da cin ƙwallo ko ɗaya ba.











