Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Arsenal ta caskara Palace ta koma ta ukun teburin Premier
Arsenal ta farfaɗo da damar lashe Premier League na bana, bayan da ta sharara 5-0 a ragar Crystal Palace ranar Asabar.
Kungiyoyin biyu sun buga wasan na hamayya a Emirtaes na mako na 21 a babbar gasar tamaula ta Ingila.
A kakar da ta wuce, Arsenal ta yi rashin nasara wasa uku daga biyar na ƙarshe da ta buga a Premier, hakan ya kai ga Manchester City ta lashe kofin.
Gunners ta buga karawar da ƙwarin gwiwa, bayan da ta je hutu a Dubai na mako ɗaya, sakamakon kammala wasannin Kirsimeti da na sabuwar shekara.
Arsenal ta hada maki ukun da take bukata, bayan da Dean Henderson ya ci gida da wadda Leandro Trossard da Gabriel Martinelli suka ci.
Tun a minti na 45 din farko Gabriel ya fara cin kwallo a minti na 11 da fara wasa daga baya ya kara na biyu.
Crystal Palace ta yi kokarin rage kwallayen, amma ba ta samu damar zura kwallo ba a raga.
Da wannan nasarar Arsenal ta koma ta uku da tazarar maki biyu tsakaninta da Liverpool ta daya.
Maki iri daya da na Manchester City ta biyu, wato 43, sai dai Arsenal ta yi karawa 21, yayin da Liverpool da Man City kowacce ta buga 20.
Palace tana mataki na 14 a teburin da maki 21, bayan karawa 21.
Ranar Lahadi za a ci gaba da fafatawa tsakanin Sheffield United da West Ham United da na Bournemouth da Liverpol.