Abin da ya sa Canada ke shirin karɓar 'yan ci-rani miliyan daya da rabi

Ɗaya cikin huɗu na mutanen Canada sun je ƙasar ne a matsayin baƙi

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Canada ta dogara kan 'yan ci-rani domin cike wagegen gurbi na tattalin arziƙi saboda mutanen ƙasar da ke ritaya daga aiki - sai dai ba kowa ne ke goyon bayan shirin shigo da baƙin ba.

A farkon wannan wata ne gwamnatin ƙasar ta sanar da shirinta na karɓar baƙi 500,000 duk shekara, kimanin baƙi miliyan 1.5 ke nan a cikin shekara uku.

Hakan na nufin Canada za su karɓi baƙi waɗanda yawansu ya ninka yawan waɗanda Amurka ke karɓa sauhuɗu.

To amma wata ƙuri'ar jin ra'ayi da aka yi a kwanan nan ta nuna cewa ba kowa ne hankalinsa ya kwanta da tsarin ba.

Canada ta yi haɗama

A tsawon shekaru, Canada ta yi ta ƙoƙarin janyo baƙi zuwa cikin ƙasar waɗanda za su yi zaman dindindin. da waɗanda za su zo su zauna tare da aiki a ƙasar, amma ba ƴan ƙasa ba - domin ci gaban tattalin arziƙinta. A bara, ƙasar ta karɓi baƙi masu aniyar zama na dindindin har 405,000, wanda shi ne mafi yawa a tarihinta.

Dalilin a bayyane yake, kamar da dama daga cikin ƙasashen turai, mafi yawan al'ummar ƙasar sun shiga shekarun tsufa kuma ba su haihuwa sosai.

Abin da hakan ke nufi shi ne, matuƙar ƙasar tana son ta ci gaba, to dole ne ta kawo baƙi.

Bayanan gwamnati sun ce a yanzu haka baƙi ne suka mamaye ɓangaren ƙwadugo a ƙasar, kuma ana sa ran baƙin za su zamo ginshiƙin haɓɓakar yawan al'ummar ƙasar nan da 2032.

A farkon wannan wata ne gwamnatin ƙasar ta sanar da cewa nan da 2025 suna sa ran karɓar baƙi 500,000 a kowace shekara, ƙarin kashi 25% ke nan a kan yawan baƙin da suka shiga ƙasar a 2021.

Ƙasar da ta sha banban da saura

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A yanzu, kowane mutum ɗaya cikin huɗu na mutanen Canada baƙo ne, ƙasa mafi yawan baƙi a cikin manyan ƙasashen duniya bakwai (G7).

Kashi 14% na al'ummar Amurka ne baƙi, haka nan ma a Birtaniya.

Madeleine Sumption, darakta a cibiyar lura da shige da ficen al'umma a jami'ar Oxford, ta ce hakan ba yana nufin Birtaniya na baya ne a harkar karɓar baƙi ba. Birtaniya, wadda ƙaramin tsibiri ne, tana da yawan al'ummar da ta ninka ta Canada sau biyu, amma tana da cunkoson al'umma.

Ita kuwa Canada wadda ke da yawan al'umma kimanin miliyan 38, da girman asa mai yawa, al'ummarta na da damar faɗaɗa.

Ta ce "ita Birtaniya ba ta samar da wata manufa ta ƙara yawan al'ummarta kamar yadda Canada ta yi ba."

Geoffrey Cameron, masanin siyasa a jami'ar MacMaster, ya ce yayin da ƙasashe irin su Canada ke fuskantar raguwar yawan haihuwa da kuma al'ummar da ke shiga shekarun tsufa, nasarar harkar shigo da baƙi ta dogara ne a kan goyon baya daga al'umma.

Ya ce "abin da ya sa wasu ƙasashen ba su iya faɗaɗawa shi ne saboda rashin goyon baya daga al'ummarsu."

Wasu da aka bai wa takardar zama ƴan ƙasar Canada

Asalin hoton, Getty Images

A yankuna daban-daban na Canada, mutane na da ra'ayoyi daban-daban kan shigara baƙi a ƙasar.

A lokacin da gwamnatin ƙasar ta bayyana sabuwar aniyarta ta karɓar baƙi, lardin Quebec, wanda ke da nasa dokokin na karɓar baƙi, ya ce ba zai karɓi baƙin da suka wuce 50,000 a duk shekara.

Hakan na nufin, Quebec wanda ke ƙunshe da kashi 23% na al'ummar ƙasar zai karɓi kashi 10% ke nan na yawan baƙin da za su iso.

Firimiyan Quebec Francoise Legault ya ce yana tsoron cewa baƙi za su nakasa harshen Faransancin da yankin ke amfani da shi.

Ya ce "shigowar baƙi 50,000 ma, ba za ka iya hana illar da hakan ke yi wa faransanci ba."

Wani jin ra'ayin al'umma ya nuna cewa uku, cikin mutum huɗu na al'ummar Canada na ɗari-ɗari kan cewa yawan shigowar baƙin zai ta'azzara matsalar ƙarancin gidaje da sauran abubuwan more rayuwa a ƙasar. Kusan rabi, wato kashi 49% sun ce baƙin da gwamnati ke so ta karɓa sun yi yawa, sai kuma kashi 31% na cewa hakan ya yi daidai.

Wani ɓangare da Canada ta sha banban da wasu ƙasashen game da batun baƙi shi ne yadda take mayar da hankali kan tattalin arziƙi - fiye da rabi na masu shiga Canada da nufin zama ana maraba da su ne saboda irin ƙwarewar da suke da ita, ba domin zuwa wurin iyalansu ba.

Ko Canada za ta cimma burinta?

Baya ga karɓar baƙin ma'aikata fiye da sauran manyan ƙasashe, ƙasar tana daga cikin waɗanda suka fi karɓar ƴan gudun hijira, inda ta karbi mutum 20,428 a 2021.

To amma yayin da ƙasar ta yi wannan hasashe, tarihi ya nuna cewa ba a kodayaushe ne take cimma irin wannan hasashe ne. Canada na son ta tsugunar da mutum 76,000 nan da 2023.