Abin da ya sa IPMAN ke son a yi karin kuɗin fetur a Najeriya

Asalin hoton, Getty Images
Kungiyar dalilan man fetur ta kasa a Najeriya, IPMAN, ta bukaci a yi karin kudin man fetur a hukumance muddin ana so a saukaka wahalhalun samun mai da kuma kawo karshen karancinsa a faɗin kasar.
IPMAN ta yi wannan kira ne a daidai lokacin da ‘yan kasar ke cigaba da fuskantar karancin mai a galibin jihohin arewa da babban birnin tarayyar ƙasar, Abuja.
An kwashe 'yan makonni ana fama da karancin man fetur, duk da irin matakan da gwamnati ke cewa tana ɗauka domin saukaka matsalar.
Kusan tun a farkon wannan shekara zuwa wannan lokaci ba a daukar wani dogon lokaci ba tare da an faɗa cikin karancin fetur ba a Najeriya.
Wannan ne ya sa farashin ya sauya a cikin watanni baya, abin da ya kawo sauki a wancan lokaci. Sai dai makonni bayan hakan sai wahalar ta sake kunno kai kuma har yanzu ana cikinta.
Me IPMAN ke cewa?
A tattaunawarsa da BBC shugaban kungiyar IPMAN reshen arewacin Najeriya, Bashir Dan-Mallam, ya ce dama fargabarsu ita ce fitowa su faɗi gaskiya.
A cewarsa suna shan matukar wahala kan abubuwan da ke faruwa, saboda man na da wahalar ɗaukowa tun daga jirgin ruwa zuwa yankunan da ya kamata.
Ya ce akwai jihohin kudu da ke sayar da man tsakanin naira 189 zuwa 190, yana mai cewa babu yadda za a yi a dauko shi zuwa arewa sannan a sayar kan kasa da wannan farashin.
Sannan ya bayyana cewa farashin gwamnati N169 ne, sai dai kuɗaɗen da ake kashewa har a kai ga kai fetur gidan mai na kai wa N194 kan kowacce lita.
Don haka idan suka sayar da ita kasa da 194 sun yi asara.
Dan-Mallam ya ce ba wai man ba ne babu ba, amma hanyoyin kawo man da kuɗaɗen da ake kashewa ne ke wahalarwa.
Kari ne kawai mafita?

Asalin hoton, Getty Images
A watanni baya an samu karin kuɗin mai lokacin wani wahala fetur mai tsananin gaske da aka shafe wata da watanni, sai dai Bashir Dan-Mallam ya ce ai abubuwa sauyawa suke yi a kullum.
Saboda harkar fetur ana yi ne don riba, ba wai mutum ya rinƙa tafka asara ba.
BBC ta tambaye shi ko anya kuwa suna adalci kan batun farashin fetur?
Ya bada amsa da cewa; "to mafita ita ce a soma janye kudin tallafin kaɗan-kaɗan ko kuma a yi karin kuɗin a hukumance".
Dan-Mallam ya ce ai komai yanzu ya sauya a duniya baki ɗaya ga kuma yadda farashin dala ke kasancewa, don haka ba wai laifinsu ba ne.
IPMAN dai na ganin akwai bukatar a zauna tsakanin hukumomi masu kayyade farashi da kuma ɓangaresu na 'yan kasuwa don sake nazarin yadda farashin zai kasance.
Sai dai sanarwar da shugabanta na kasa ya fitar na cewa dole farashin a hukumance ya kai 200 zuwa 210 kafin a soma ganin saukin wahalhalun man.
Matsalolin da ake shiga idan ana karancin fetur
A duk lokacin da 'yan Najeriya suka shiga karancin fetur ana samun tarin matsaloli kama daga samun dogayen layuka a gidajen mai da kuma sayen man da matuƙar tsada.
Wata matsala ta biyu da al'umma ke kokawa a kanta ita ce ta yadda masu ababen hawa suka ƙara farashi.
A wasu wuraren ma ba farashin abin hawa ne kawai ya yi tashin gwauron zabi ba, har da na wasu abubuwan yau da kullum.
Sannan a wasu wuraren ma sai dai a sayi mai a hannun ƴan bumburutu, wadanda suke nunka kudin kowace lita sau uku ko huɗu kan yadda aka saba saya.
Karin haske
Najeriya ita ce ƙasar da ta fi kowacce arziƙin man fetur a Afirka, sai dai an shafe gwaman shekaru tana fama da samun matsalar ƙarancin man fetur akai-akai.
Hakan ya samo asali ne kan rashin matatun man fetur da ke cikin hayyancinsu a ƙasar.
Wannan ne dalilin da ya sa a dole ƙasar ke sayo tataccen man fetur daga ƙasashen wajen da take sayar musu da ɗanyen.
Batun shirin gwamnati na janye bayar da tallafin mai yana yawan jawo tarnaƙi a wajen samar da man.
A baya ana dangana tarin wasu matsalolin na daban idan ana cikin wahalar mai. Sai dai a wannan lokaci kusan a fili yake cewa kari ko janye tallafi ne ke nema zama mafita.
'Yan Najeriya dai sun zura ido domin ganin yadda za ta kaya, musamman a wannan lokaci da manyan zabuka ke tunkaro kasar.












