Yadda lalacewar titunan birnin Kano ke ci wa mutane tuwo a kwarya

Bayanan bidiyo, Danna hoton da ke sama domin kallon bidiyon:
Yadda lalacewar titunan birnin Kano ke ci wa mutane tuwo a kwarya
An wallafa

A birnin Kano, ma fi yawan jama’a a arewacin Najeriya na fama da rashin kyawun tituna musamman titunan cikin unguwanni da wadanda suka hada manyan hanyoyi.

Gwamnatoci dai na cewa birnin yana da girman da hade shi da tituna na da matukar wuya.

Daga shekarar 1999 ne dai bayan komawa mulkin dimokradiyya tituna suka fara yalwata a birane ciki har da na Kano.

Sai dai wata matsala da ta fito fili dangane da batun tituna a Kano ita ce yadda kusan kowacce gwamnati da ta hau mulki take kashe kudade domin sake gina titunan da gwamnatin da ta shude ta gina.

Masana na alakanta hakan da rashawa da cin hanci da ke baibaye da harkar kwangilar tituna wadanda ake gina su ba tare da inganci ba.

Har wa yau, rashin tsarin kyawawan magudanun ruwa kan haifar da ambaliya a kan tituna wani abu da ke taimakawa sosai wajen kwaye kwalta ya kuma haifar da ramuka.

To sai dai gwamnati mai ci ta ce tana duba yiwuwar gina sabbin hanyoyi da za ta shigar a kasafin kudin shekara mai kamawa.