Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An yi watsi da tayin Arsenal kan Calafiori, Araujo da Raphinha za su bar Barca
An yi watsi da tayin Arsenal kan Riccardo Calafiori, Manchester United za ta tattauna kan neman Bruno Fernandes kungiyoyi ke yi. Real Madrid na zawarcin William Saliba.
An yi watsi da tayin da Arsenal ta yi na Yuro miliyan 47 kan dan wasan baya Riccardo Calafiori daga Bologna, inda ake neman akalla euro miliyan 50 kan dan wasan na Italiya. Chelsea ma zawarcin dan wasan mai shekaru 22. (Corriere dello Sport)
Manchester United za ta tattauna kan neman da kungiyoyi ke yi wa kyaftin dinta Bruno Fernandes, mai shekara 29, amma ana sa ran dan wasan tsakiyar na Portugal zai ci gaba da zama a kungiyar tare da sanya hannu kan wata sabuwar yarjejeniya. (Mirror)
An hango Dele Alli yana atisaye tukuru a horo yayin da yake kokarin neman sabon kulob bayan barin Everton lokacin da kwantiraginsa ya kare a karshen kakar wasan da ta gabata. (Express)
Dan wasan bayan Faransa William Saliba zai iya barin Arsenal a bazara, inda Real Madrid ke zawarcin dan wasan mai shekaru 23. (Mirror)
Ana sa ran dan wasan Napoli Victor Osimhen, mai shekara 25, zai buga wasannin share fage a mako mai zuwa, a daidai lokacin da Manchester United da Chelsea da kuma Arsenal ke zawarcin dan wasan na Najeriya. (Football Italia)
West Ham na tunanin mka sabon tayi, kan dan wasan bayan Nice Jean-Clair Todibo bayan ta yi watsi da tayin fan miliyan 24.5 kan dan wasan na Faransa mai shekaru 24. (Mail)
Barcelona na kokarin siyan dan wasan gaba na kasar Sipaniya Dani Olmo daga RB Leipzig, inda kungiyar ta kasar Sipaniya ke kokarin amincewa da shirin biyan kudin dan wasan mai shekaru 26 da haihuwa kan Yuro miliyan 60 (90 Min)
Dan wasan gefe na Brazil Willian ya ki amincewa da tayin sabon kwantiragi a Fulham, inda kungiyoyi a Saudi Arabiya da Turkiyya ke zawarcinsa (Mail)
Dan wasan tsakiya na Paris St-Germain Ethan Mbappe, dan uwan kyaftin din Faransa Kylian, na shirin kulla yarjejeniya ta dogon lokaci a Lille, dan wasan mai shekaru 17 bai taba tattaunawa daReal Madrid ba saboda dan kasar Faransar yana son ci gaba da zama a Ligue. 1. (Fabrizio Romano)
Everton na sha'awar dauko dan wasan Kamaru Jackson Tchatchoua, mai shekara 22, yayin da Hellas Verona ta Italiya ke son dan wasan bayan kan kusan Euro miliyan 8 (TuttoMercatoWeb)
Atalanta na shirin dauko dan wasan tsakiya na Italiya Nicolo Zaniolo a matsayin aro daga kungiyar Galatasaray ta Turkiyya (Gazzetta dello Sport)
Barcelona za ta yi niyyar siyar da dan wasan baya na Uruguay Ronald Araujo da dan wasan Brazil Raphinha a bazarar nan domin dauko dan wasan gaba na Athletic Bilbao da Spain Nico Williams, mai shekara 21, zuwa Camp Nou. (SportsMole)
Chelsea na zawarcin dan wasan baya na Nottingham Forest Murillo amma suna ganin farashin dan kasar Brazil din mai shekaru 21 da haihuwa ya yi tsada sosai. (Football London)
Ana hasashen dan wasan bayan AC Milan Theo Hernandez zai kammala komawa Manchester City kan fan miliyan 51, inda a halin yanzu dan wasan mai shekaru 26 ke taka leda a Faransa a gasar Euro 2024. (Manchester Evening News)
Dan wasan tsakiya na Chelsea Conor Gallagher zai yi "jinkirin" komawa Aston Villa yayin da dan Ingilan mai shekaru 24 ke jiran sabuwar yarjejeniya da Blues. (Telegraph)