Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Liverpool ta dage kan Gordon, City ta doke Arsenal a zawarcin McAidoo
Liverpool ta ƙwallafa ranta a kan Anthony Gordon, amma kuma Newcastle ta kafe cewa ɗan wasan na gaba na gefe ɗan Ingila mai shekara 23 ba na sayarwa ba ne. (Telegraph)
Duk da matsayar da ƙungiyar tasa ta bayyana ana ganin Liverpool za ta ƙara matsa ƙaimi domin ganin ta shawo kan Newcastle ɗin ta sayar mata da shi a bazaran nan. (Teamtalk).
Manchester City ta kasa Arsenal a zawarcin matashin ɗan wasan tsakiya na Chelsea Ryan McAidoo, ɗan Ingila mai shekara 16. (Mirror).
Ita kuwa Manchester United ta yi wa ɗan bayan Netherlands Matthijs de Ligt, tayin kwantiragin shekara biyar ne, yayin da take ci gaba da tattaunawa da Bayern Munich a kan ɗan wasan mai sheakara 24. (De Telegraaf - in Dutch).
Haka kuma United ɗin za ta ƙara gabatar da buƙatarta ta sayen Jarrad Branthwaite idan Everton ta rage kuɗin da ta sanya masa, to amma ƙungiyar ba ta cikin wani matsi na buƙatar kuɗi da zai sa lalle ta sayar da matashin ɗan bayan na Ingila mai shekara 22. (Sky Sports)
Ɗan gaban Galatasaray Wilfried Zaha na son komawa gasar Firimiya inda West Ham, da Wolves da ma tsohuwar ƙungiyarsa Crystal Palace, suke sha'awar ɗan Ivory Coast ɗain mai shekara 31. (Star).
Wata kungiyar babbar gasar Saudiyya na tattaunawa da Newcastle, a kan sayen ɗan wasan gaba na Paraguay Miguel Almiron. (Sky Sports).
Arsenal na shirin sayen mai tsaron ragar Sifaniya David Raya, mai shekara 28, dindindin daga Brentford, bayan da ta karɓi aronsa a kakar da ta wuce. (Mail).
Liverpool da AC Milan na son ɗan wasan tsakiya Adrien Rabiot, ɗan Faransa, bayan da kwantiraginsa da Juventus ya ƙare. (Calciomercato).
Sevilla za ta karɓi aron ɗan wasan tsakiya na Arsenal Albert Sambi Lokonga, ɗan Belgium, tsawon kaka ɗaya. (Teamtalk).
Southampton za ta gabatar da tayin fam miliyan 20, a kan ɗan wasan tsakiya na Celtic, Matt O'Riley, na Denmark . (Talksport).
Brighton, da Brentford, da Everton da kuma Southampton dukkanninsu suna sha'awar matashin ɗan wasan tsakiya na Millwall, Josh Stephenson, ɗan Ingila mai shekara 18. (Football Insider).
Newcastle United ta dage kan riƙe ɗan gabanta Alexander Isak, yayin da rahotanni ke danganta tafiyar ɗan Sweden ɗin Arsenal ko Chelsea. (Football London).
Ana sa ran Nottingham Forest ta rabu da ɗan wasanta na tsakiya Lewis O'Brien, ɗan Ingila a bazaran nan, inda Sheffield United, da Preston North End da Ipswich Town suke sha'awarsa. (Northamptonshire Live)