Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Arsenal ta barar da maki biyu a gidan Southampton
Southampton da Arsenal sun tashi 1-1 a wasan mako na 13 a gasar Premier League da suka buga ranar Lahadi a St Mary.
Arsenal wadda ke jan ragamar teburin Premier ta fara cin kwallo ta hannun Granit Xhaka a minti na 11 da fara wasa.
Sai dai Southampton ta farke ta hannun Stuart Armstrong bayan da aka koma zagaye na biyu.
Wannan shi ne karon farko da Gunners ta buga 1-1 a Premier League a kakar bana a karawa 11, bayan da ta yi nasara a tara, Manchester United ta doke ta 3-2.
Da wannan sakamakon Arsenal ta ci gaba da zama ta biyu a teburin babbar gasar tamaula ta Ingila da maki 28 da tazarar maki biyu tsakani da Manchester City ta biyu.
Southampton wadda ta yi wasa 12 ta ci gaba da zama a mataki na 15 da makinta 12.
Sakamakon wasan da suka kara a tsakaninsu a bara:
2021/2022
Premier League Asabar 16 ga watan Afirilun 2022
- Southampton 1 - 0 Arsenal
Premier League Asabar 11 ga watan Disambar 2021
- Arsenal 3 - 0 Southampton
Wasu batutuwa da ya kamata ku sani kafin wasan Southampton da Arsenal
Southampton
Ranar Laraba Southampton ta yi nasara a kan Bournemouth da ci 1-0, shi ne karon farko da kungiyar ta yi daga 17 kwallo bai shiga ragarta ba, tun bayan doke Arsenal 1-0 a cikin watan Afirilu.
Kungiyar na fatan cin wasa biyu a jere a Premier, rabon da ta yi hakan tun cikin Fabrairu a lokacin da ta yi nasara a kan Everton da Norwich City a jere.
Kungiyar da Ralph Hasenhuttl ke jan ragama an zura mata kwallo 249 a babbar gasar tamaula ta Ingila karkashin shi - tazarar kwallo 30 fiye da kowacce kungiya.
Arsenal
Arsenal ta yi kan-kan-kan a bajintar cin wasa tara daga 10 a Premier League mafi kayatarwa kenan, kamar yadda ta yi bajinta a 1903/04 a rukuni na biyu.
Gunners ta yi nasara a wasa hudu a jere a dukkan fafatawa a karon farko tun biyar da ta ci tsakanin Satumba zuwa Oktoban 2018
Arsenal ce wadda ba a ci kwallaye da yawa a wasannin waje da take yi a kakar nan, uku ne suka shiga ragarta, sannan ta yi wasa hudu ko daya bai shiga raga ba.
Haka kuma Arsenal ita ce tilo da ta zura kwallo a raga a dukkan wasan Premier da ta yi a bana, ba wadda ta yi wannan kwazon kawo yanzu.