Me kuke son sani kan wasan Netherlands da Argentina?

Asalin hoton, Getty Images
Ranar Juma'a za buga fafatawar Quarter finals tsakanin Netherlands da Argentina a filin wasa na Lusail a Gasar Kofin Duniya da ake yi a Qatar.
Wannan shine karo na 10 da za a yi tata burza tsakanin Netherlands da Argentina, bayan haduwa biyar a Gasar Kofin Duniya,
Kuma Netherland ce ta ci hudu Argentina ta yi nasara a daya da canjaras hudu a tsakaninsu.
Wasa na karshe da suka hadu shine a kofin duniya a 2014 inda suka tashi ba ci aka yi karin lokaci ba a fidda gwani ba, amma Argentina ta ci 4-2 a bugun fenariti.
Netherlands wadda bata taba lashe Kofin Duniya ba na fatan kai wa daf da karshe karo na hudu, bayan 1998 da 2010 da kuma 2014 .
Ita kuwa Argentina mai kofin duniya biyu na fatan kai wa daf da karshe karo na biyar, bayan 1930 da 1986 da 1990 da kuma 2014.
Argentina ta kawo wannan matakin a wasannin Qatar, bayan da ta ja ragamar rukuni na shida da maki shida mai dauke da Saudi Arabia da Poland da kuma Mexico.
Ranar Asabar Argentina ta yi nasara a kan Australia da ci 2-0 a wasan zagaye na biyu.
Ita kuwa Netherlands ta yi ta daya a rukunin farko da maki bakwai, mai dauke da Senegal da Ecuador da kuma Qatar mai masaukin baki.
A wasan zagaye na biyu Netherlands ta ci Amurka 3-1 ranar Asabar.
Jerin wasa tsakanin Netherlands da Argentina:
Gasar Kofin Duniya Laraba 9 ga watan Yulin 2014
- Netherlands 0 - 0 Argentina
Gasar Kofin Duniya Laraba 21 ga watan Yunin 2006
- Netherlands 0 - 0 Argentina
Wasan sada zumunta Laraba 12 Febrairun 2003
- Netherlands 1 - 0 Argentina
Wasan sada zumunta Laraba 31 ga watan Maris 1999
- Netherlands 1 - 1 Argentina
Gasar Kofin Duniya Asabar 4 ga watan Yulin 1998
- Netherlands 2 - 1 Argentina
Wasan sada zumunta Talata 22 ga watan Mayun 1979
- Argentina 0 - 0 Netherlands
Gasar Kofin Duniya Lahadi 25 ga watan Yunin 1978
- Argentina 3 - 1 Netherlands
Gasar Kofin Duniya Laraba 26 Yunin 1974
- Netherlands 4 - 0 Argentina
Wasan sada zumunta Lahadi 25 ga watan Mayun 1974
- Netherlands 4 - 1 Argentina











