Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abin da ya sa sabon shugaban Kenya William Ruto ya dauki matakin zaftare tallafi kan fetur
A yayin da shugabanni a kasashe duniya suke bijiro da shirye-shiryen rage radadin talauci ga al'ummarsu, shi kuwa sabon shugaban kasar Kenya, William Ruto a matakin farko da ya dauka, ya bai wa kowa mamaki inda ya cire tallafin man fetur lamarin da ya sa yanzu ake sayar da fetur din a farashi mafi girma da ba a taba yi ba a kasar.
Wannan mataki ya sa mutane sun soma korafi musamman a shafukan sada zumunta, yayin da su kuma masu sharhi suka yi gargadin cewa yana iya rasa goyon bayan da yake samu tun ma yanzu da ya soma mulkinsa, bayan ya lashe zabe da kyar a watan jiya.
"Tun watannin da suka gabata na daina amfani da motata domin zuwa ofis kuma yanzu ina cike da damuwar ganin cewa su kansu motocin haya za su yi tsada idan suka kara kudin mota," a cewear wani mazaunin birnin Nairobi John Maina a hirarsa da BBC.
Shugaba Ruto ya yi yakin neman zabensa ne kan alwashin kyautata rayuwar 'yan kasar marasa karfi, da kirkiro ayyukan yi da rage radadin rayuwa, yana mai jaddada cewa shi ma dan talakawa ne.
Daya daya cikin abubuwan da ya yi alkawarin aiwatarwa shi ne cire haraji daga kan fetur da kuma rage farashin muhimman kayayyakin more rayuwa.
Sai dai a jawabinsa na farko, shugaban kasar ya sanar da cire tallafin da ake yi kan muhimman abubuwa, yana mai cewa tallafin zai lakume $2.3bn (£2bn) zuwa karshen shekarar kudi mai zuwa, wato watan Yunin 2023.
"Wannan kudin ya yi daidai da dukkan kasafin kudin gwamnati," in ji shi, yana mai cewa tallafin bai biya bukatun rage radadin rayuwa da aka sanya shi domin su ba.
Masana tattalin arziki sun amince cewa Kenya ba za ta iya jure wa biyan tallafi ba kuma tallafin wata hanya ce da mutane ke amfani da ita wajen wawurare kudaden gwamnati sai dai sun ce a mataki na kankanen lokaci, 'yan kasar Kenya za su ji radadin karin kudin fetur da kimanin kashi 13 cikin 100 inda yanzu ake sayar da kowacce lita a kan $1.49.
Sai dai masu sharhi sun yi gargadin cewa cire tallafin man fetur din zai yi wa shugaban kasar illa a fannin siyasa.
"Tabbas mutane za su ji radadin cire tallafin domin kuwa kusan farashin komai sai ya tashi ," in ji Herman Manyora a tattaunawa da BBC.
Ya ce ba a bukatar yin hanzari wajen daukar babban mataki irin wannan tun ma kafin a kafa gwamnati saboda za a rika kallon batun a matsayin "matakin da mutum daya ya dauka maimakon wanda gwamnati baki daya ta yi nazari a kansa kafin a dauka".
Ya zuwa wannan lokaci Shugaba Ruto bai nada ministoci ba, wadanda sai majalisa ta amince da su kafin su soma aiki.
Mai sharhi Javas Bigambo ya ce kamata ya yi a Mr Ruto ya soma da yi wa 'yan kasar Kenya bayani kan muhimmancin cire tallafin, da kuma bukatar yin amfani da kudin wajen ayyukan more rayuwa.
Mr Ruto ya ce ba zai sabunta batun cire tallafi ba wanda ya rage farashin kayan abinci rin su masara da garin fulawa da kusan rabi, wanda aka kaddamar ana dab da gudanar da babban zaben kasar.
A halin da ake ciki Kenya tana da kangin basussuka kuma Asusun Bayar da Lamuni na Duniya ya gindaya mata sharadin cewa dole ta cire tallafin mao, wanda asusun yake gani a matsayin wani "koma-baya".