Arsenal ta kara gwada wa Real ƙwanji a Champions League?

Champions League

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Arsenal ta ɗura 3-0 a ragar Real Madrid a wasan farko zagayen kwata fainal a Champions League ranar Talata a Emirates.

Ƙungiyoyin sun tashi ba ci a minti na 45 ɗin farko, sai da suka koma zagaye na biyu ne bayan shan ruwa Gunners ta zura uku a raga.

Declan Rice ne ya fara cin na farko, sannan ya kara na biyu minti 12 tsakani duk daga bugun tazara, sai Mikel Merino ya kara na uku, saura minti 15 a tashi wasan.

Kenan Rice ya zama na farko da ya ci ƙwallo biyu a bugun tazara a ziri ƙwale a Champions League.

Real ta karasa karawar da ƴan wasa 10 a cikin fili, bayan da aka bai wa Eduardo Camavinga jan kati.

Wannan shi ne karo na biyu da suka kece raini a tsakaninsu a gasar zakarun Turai, inda Gunners ta ci 1-0 a Sifaniya a kakar 2005/06, sannan suka tashi ba ci a Sifaniya a wasa na biyu.

Wasa biyu da aka kara tsakanin Arsenal da Real a Champions League:

Champions League ranar Laraba 8 ga watan Maris 2006

  • Arsenal 0 - 0 Real Madrid
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Champions League ranar Talata 21 ga watan Fabrairun 2006

  • Real Madrid 0 - 1 Arsenal

Ranar Laraba 16 ga watan Afirilu, Real Madrid za ta karɓi Arsenal a wasa na biyu a Champions League zagayen kwata fainal a Santiago Bernabeu.

Gunners ta kawo wannan matakin, bayan da ta fitar da PSV Eidhoven, ita kuwa Real ta yi waje da Atletico Madrid a zagaye na biyu a gasar.

Real Madrid mai rike da champions League tana da 15 jimilla, yayin da Arsenal ke fatan lashe na farko a tarihi.

Rabon da Arsenal ta kai daf da karshe a Champions League tun bayan 2008/09, amma yanzu tana da damar kai wa zagayen gaba a kakar bana.

Ƴan wasan da Real Madrid ta je da su Emirates:

Masu tsare raga: Courtois, Fran González da kuma Sergio Mestre.

Masu tsare baya: Alaba, Lucas V., Vallejo, Fran García, Rüdiger, Asencio, Jacobo da kuma Lorenzo.

Masu buga tsakiya: Bellingham, Camavinga, Valverde, Modrić, Arda Güler da kuma Chema.

Masu cin ƙwallaye: Vini Jr., Mbappé, Rodrygo, Endrick, Brahim da kuma Gonzalo.