Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
‘Mun zama tamkar mabarata saboda halin da ƴan bindiga suka jefa mu'
Wata uwa da rikicin ƴan fashin daji ya tilasta wa zuwa gudun hijira a jihar Katsina ta ce rikicin ya yi matuƙar shafar rayuwar ‘ya’yansu, inda har ɗan yayenta ya kamu da tamowa (cutar yunwa).
Jamila Sani ta ce ɗan nata ba ya samun abinci mai gina jiki saboda a yanzu ana fama ne kawai a samu abin da za a ci (ba lallai sai mai daɗi ko mai gina jiki ba).
Wasu alƙaluma sun ce ƙananan yara sama da miliyan huɗu ne ke fama da matsanancin rashin abinci mai gina jiki bana a arewacin Najeriya.
Jamila Sani ta ce rayuwarsu ta tagayyara ne tun lokacin da ɓarayin daji suka addabe su da hare-hare a ƙauyensu na Ɗan Geza, lamarin da ya tilasta musu tserewa zuwa Batsari.
“Mun dawo Batsari, gidan da muke ci ya zube. Muka taho da dabbobi, ɓarayi suka biyo mu (har) cikin gida ni da mijina, suka ritsa mu da bindiga, suka kore. Noma ya gagara, zaman gida ya gagara, dole ya tafi can (ci-rani), ɗan abin da ya samu ya aiko mana.”
Mahaifiyar wadda ta ce daga Batsari sun sake bazama zuwa birnin Katsina gudun hijira, ta ce ta kai ɗanta asibiti ne bayan jikinsa ya yi ta kumburi jim kaɗan da yaye shi.
Ta ce su mazaunan ƙauye ne kuma a baya, ba su taɓa shiga matsala irin wannan ba, idan damuna ta yi nisa, sukan sayar da hatsinsu ne, su samu ‘yan kuɗaɗe don zaman gari, “amma bana bara ce kaɗai ba mu yi ba”.