Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Hira da mai ɗakin gwamnan Katsina
Hira da mai ɗakin gwamnan Katsina
An wallafa
Hajiya Fatima Dikko Radda, mai ɗakin gwamnan jihar Katsina, ita ce shugabar wata gidauniya da ke yaƙi da cutar sankarar mata da ta mahaifa.
Ta ce a yanzu baban aikin da ta sa a gaba shi ne yaƙi da cutar sankarar mama da ta mahaifa, kasancewa cutar sankarar mama ce ta yi ajalin mahaifiyarta, kamar yadda ta shaida wa BBC.
Kan haka ne ta sha alwashi yaki da cutar, don kare 'yan'uwanta mata daga kamuwa da cutar.
Ta kuma ce burinta shi ne ci gaba da aiki da gidauniyarta domin wannan aiki, da kuma inganta ilimin 'ya'ya mata.