AC Milan ta ɗauki Conceicao sabon kociyanta

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

An naɗa tsohon kociyan Porto, Sergio Conceicao a matakin sabon mai horar da AC Milan, bayan da ta kori Paulo Fonseca.

Kociyan tsohon ɗan wasan Lazio da Inter Milan da Parma ya saka hannu kan yarjejeniyar wata 18 da ƙungiyar ta San Siro.

Conceicao, mai shekara 50, ya lashe manyan kofi 11 a kaka shida a Porto daga baya ya ajiye aikin a karshen kakar da ta wuce.

Zai fara aiki ranar 3 ga watan Janairu a wasan hamayya tsakanin Milan da Juventus a wasan farko a daf karshe a Italian Super Cup.

A wasan ne Conceicao zai fuskanci ɗansa Francisco, wanda ke taka leda a Juventus.

Milan ta raba gari da Fonseca ranar Litinin da safe awannin tsakani bayan 1-1 da Roma.

Hakan ya sa wadda take da kofin zakarun Turai bakwai take ta takwas a teburin Serie A da tazarar maki 14 tsakani da waɗanda ke jan ragama Atalanta da Napoli.

Fonseca ya maye gurbin Stefano Pioli cikin watan Yuni.

Milan tana ta 12 a ƙungiya 36 da ke buga sabon fasalin Champions League, bayan rashin nasara biyu da cin wasa huɗu daga shidan da ta fafata.