Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An yi waje da AC Milan daga Champions League na bana
An yi waje da AC Milan a Champions League, bayan tashi 1-1 da Feyenoord a wasa na biyu na cike gurbi da suka kara a San Saro ranar Talata.
Tun a makon jiya aka ci Milan 1-0 a Netherlands, wadda ta fara zura ƙwallo a dakika ta 36 da fara tamaula ta hannun Santiago Gimenez.
Ta zama ƙwallon da aka ci a karancin lokaci a Champions League a tarihi - daga baya Feyenoord ta farke ta hannun Julian Carranza.
Koda yake Milan ta karasa wasan da ƴan ƙwallo 10 a cikin fili, bayan da aka bai wa Theo Hernandez jan kati.
Haka kuma an bai wa ɗan wasan Feyenoord, Givairo Read jan kati - kenan An yi waje da Milan da cin 2-1 gida da waje.
Ranar Juma'a za a raba jadawalin zagayen ƴan 16, watakila Feyenoord ta fuskanci Inter Milan ko kuma Arsenal a watan Maris.