Kayatattun hotunan Afirka na mako daga 29 ga Yuli - 4 ga Augusta 2022

Senegal

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Ranar Juma’a magoya bayan gamayyar jam’iyyun siyasa ta Shugaba Macky Sall suna mara wa dan takararsu , Youssoupha Niang, baya gabanin zaben majalisar dokoki a wani gangami a Dakar, babban birnin kasar
An wallafa
Kenya

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A wannan taro wasu mata sanye da farar riga da wando mai launin hoda sun rika waka da rawa
Senegal

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A ranar Lahadi lokacin da ake gudanar da zaben, wasu maza sun zauna a wajen wata rumfar zabe a Ngor Dakar
South Afrika

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,  'Yar wasan Tennis ta kasar Afrika ta Kudu Zodwa Maphangain ta mayar da hankali sosai a wasan da aka yi  a Birmingham, na Ingila a ranar Laraba a wasannin motsa jiki na Commonwealth
Common wealth

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, 'Yar wasan Najeriya Chioma Onyekwere a zagayen karshe na wasan jefa dalma
Wasan Commonwealth

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, 'Yar wasan kasar Afrika ta Kudu Shante Koti a yaytin da take wasan motsa jiki
Masar

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Jiragen saman yakin Masar sun yi wasa a saman Dala a ranar Laraba .
Masar

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A kasa kuwa  wadannan mazan sanye da tufafin gargajiya na Masar sun rika busa sarewa
Uganda

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Mamakon ruwan sama a gabashin Uganda ya sanya koguna sun batse a ranar Litinin inda aka dauki hotunan mutane da ke kokarin zakulo gawarwarkin mutane daga cikin  wata karamar motar safa a Namakwekwe...
Wasu mutane suka amfani da igiya wajen kokarin fito da mota daga cikin ruwa

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wasu mutane sun yi amfani da igiya wajen kokarin fito da mota daga cikin ruwa
A Algeria mawaka ne suka cashe a lokacin rufe bikin Timgad International Festival a Batna ranar Litinin...

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A Algeria mawaka ne suka cashe a lokacin rufe bikin Timgad International Festival a Batna ranar Litinin...
Wata yarinya

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Ranar Asabar wannan yarinyar a Addis Ababa, babban birnin Ethiopia, ta shiga atisaye da ake yi mako-mako na gasar zamiya ta katako mai taya da 'yan kungiyar Ethiopian Girls Skate suke yi, da zummar zaburar da kananan yara rungumar wasan.
Tsitsi Dangarembga

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Marubicuya 'yar kasar Zimbabwea Tsitsi Dangarembga tana tsaye a wajen Kotun Majistiret da ke Harare ranar Alhamis a yayin da ake tunanin daukar mataki kan ko za a yi shari'arta game da zargin harzuka mutane yayin zanga-zanga. Ta musanta aikata ba daidai ba.
Wata mace

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Wata mace tana neman sunanta a jerin sunayen masu kada kuri'a ranar Alhamis a yayin da ake shirin gudanar da zaben shugaban kasa a kasar Kenya a makon gobe