Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abu uku da zan mayar da hankali a kai idan na zama gwamnan Kaduna - Isa Ashiru
Dan takarar gwamna a Jam'iyyar PDP a Jihar Kaduna, Hon Isa Muhammad Ashiru wanda ke takara a karo na uku domin neman zama gwamnan jihar ya ce tsaro zai fi bai wa muhimmanci.
Honorabul Isa Muhammad Ashiru yana takarar neman zama gwamnan Jihar Kaduna a Jam'iyyar PDP a karo na uku.
Ya ce tsabar son ganin ya kawo sauyi a jihar ne ya sa ya nace sai ya zama gwamna.
Ya ce: "Zan mayar da hankali kan abubuwa uku da suka hada da tsaro da inganta sha'anin noma da kuma samar da ayyukan yi ga matasa."
Dangane da wasu sarakunan gargajiya da gwamnatin APC ta rushe, Isa Ashiru ya ce dole ne a koma musu "idan dai har ana son samun ingantaccen tsaro."