Me ya sa kadarorin Iran da aka riƙe ke da muhimmanci a tattaunawa da Amurka?

Tsawon shekaru, Iran na ƙoƙarin samun damar amfani da kuɗaɗenta da ke ajiye a ƙasashen waje, amma takunkuman tattalin arziki da aka ƙaƙaba mata sun hana ta samun damar.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Tsawon shekaru, Iran na ƙoƙarin samun damar amfani da kuɗaɗenta da ke ajiye a ƙasashen waje, amma takunkuman tattalin arziki da aka ƙaƙaba mata sun hana ta samun damar.
    • Marubuci, Sara Fayyad
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Arabic
    • Marubuci, Ali Ramazanian
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Mai sharhi kan tattalin arzikin Iran
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 8

Sakin kadarorin Iran da aka riƙe ko aka takaita amfani da su na ɗaya daga cikin batutuwan da suka fi jawo cece-kuce a dangantakar Iran da ƙasashen Yamma.

Wannan batu shi ne muhimmin ɓangare na yarjejeniyar zaman lafiya da ake yi tsakanin Iran da Amurka wanda kuma suka rattaba wa hannu a kwanan nan, inda hakan ke da nufin kawo ƙarshen rikicin da ya ɓarke tsakanin ƙasashen biyu.

Tsawon shekaru, Iran na ƙoƙarin samun damar amfani da kuɗaɗenta da ke ajiye a ƙasashen waje, amma takunkuman tattalin arziki da aka ƙaƙaba mata sun hana ta samun damar.

Duk da yake yawancin waɗannan kadarori ba sa cikin Amurka, amma ƙasar na taka muhimmiyar rawa wajen yanke hukuncin ko za a ba Iran damar amfani da su ko a'a.

Masu sharhi sun ce idan aka bai wa Iran damar amfani da ko da wani ɓangare ne na waɗannan kuɗaɗe, zai taimaka wa tattalin arzikinta da ya daɗe yana fama da takunkumi, hauhawar farashin kaya, faɗuwar darajar kuɗinta, da kuma illolin da rikicin baya-bayan nan da Amurka da Isra'ila ya haifar mata.

Sai dai sun yi gargaɗin cewa, ko da an cimma yarjejeniya, aiwatar da ita da kuma miƙa kuɗaɗen ba abu ne mai sauƙi ba, saboda akwai ƙalubale na shari'a da kuɗi da kuma siyasa.

To amma waɗannan irin kadarori ne, kuma ta wace hanya Iran za ta iya samun damar amfani da su cikin sauƙi?

Waɗanne irin kadarori ne?

Kadarorin Iran da aka riƙe sun haɗa da kuɗaɗen man fetur, kuɗaɗen da ta samu daga fitar da kayayyaki da kuma kuɗaɗen ajiya a bankunan ƙasashen waje

Asalin hoton, Bloomberg via Getty Images

Bayanan hoto, Kadarorin Iran da aka riƙe sun haɗa da kuɗaɗen man fetur, kuɗaɗen da ta samu daga fitar da kayayyaki da kuma kuɗaɗen ajiya a bankunan ƙasashen waje

A hukumace babu wani adadi da ke nuna jimillar kadarorin Iran da aka riƙe, amma ƙididdiga na nuna cewa za su kai tsakanin dala biliyan 27 zuwa sama da dala biliyan 100.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ba a cikin asusu guda ɗaya aka riƙe da waɗannan kuɗaɗe ba, ballantana Iran ta iya amfani da su kai tsaye. Akwai kuɗaɗen da ƙasar ta samu daga sayar da man fetur, gas da wutar lantarki, da kuma kuɗaɗen ajiya a bankunan da ke ƙasashen waje, da kuma wasu kadarorin da ake shari'a a kansu - wasu tun kafin juyin juya halin Musulunci na shekarar 1979.

Idan Iran ta sayar da man fetur a ƙasashen waje, ana ajiye kuɗin ne a asusun da ke ƙasar da ta saya. Sai dai takunkuman da aka ƙaƙaba mata sun hana ta kwashe yawancin kuɗaɗen zuwa ƙasarta.

An fara riƙe kadarorin Iran ne bayan garkuwa da jami'an ofishin jakadancin Amurka a Tehran a shekarar 1979. Duk da cewa an saki wasu kadarori bayan wata yarjejeniya da aka cimma daga baya, har yanzu ana taƙaddama kan wasu yarjejeniyar soji da aka ƙulla kafin juyin juya halin.

A tsakanin 2011 zuwa 2012 an sake sanya wa kadarorin Iran takunkumi, game da batun nukiliya tare da hana Iran amfani da wasu bankunan duniya. Takunkumin ya ƙara ƙarfi ne bayan Amurka ta fice daga yarjejeniyar nukiliyar 2015 (JCPOA) a shekarar 2018.

Yayin da takunkuman suka ƙara tsananta, adadin kuɗaɗen shigar Iran da suka maƙale a ƙasashen waje ya ci gaba da ƙaruwa. Wasu daga cikin kuɗaɗen an riƙe su gaba ɗaya, yayin da wasu kuma aka gindaya ƙa'idoji masu tsauri kan yadda za a iya amfani da su.

Masanin tattalin arzikin duniya a cibiyar Middle East Council, Frédéric Schneider, ya ce akwai kadarori daban-daban da riƙe wa Iran, waɗanda suka haɗa da kuɗaɗen da hana amfani da su gaba ɗaya, da kuma kuɗaɗen da ba za a iya dawo da su Iran ba, da kuma kadarorin da ake shari'a a kansu a kotuna.

A ina ake riƙe da kuɗaɗen Iran?

Mafi yawan kuɗaɗen Iran da aka riƙe ba sa cikin Amurka - suna ajiye ne a wasu ƙasashe.
Bayanan hoto, Muhimman wuraren da ake riƙe kadarorin Iran ko takaita amfani da su

Mafi yawan kuɗaɗen Iran da aka riƙe ba sa cikin Amurka - suna ajiye ne a wasu ƙasashe.

An yi ƙiyasin cewa mafi yawan kuɗaɗen suna ƙasar China, wadda ita ce babbar mai sayen man fetur daga Iran, inda adadin ya kai tsakanin dala biliyan 20 zuwa 50.

Sauran kuɗaɗen suna ƙasar Iraƙi, daga kuɗin iskar gas da lantarki da Iran ke fitarwa, kuma an kiyasta za su kai dala biliyan 10 zuwa 15.

A shekarar 2023 kuma, Koriya ta Kudu ta tura kusan dala biliyan shida na kuɗaɗen man fetur ɗinIran zuwa wani asusu a ƙasar Qatar.

Sai dai kuma Amurka ta bayyana cewa Iran ba za ta iya amfani da kuɗaɗen nan take ba, lamarin da ya sa suka ci gaba da zama a Qatar.

Akwai kuma wasu kuɗaɗen Iran da aka riƙe a ƙasashe kamar India, Japan da Luxembourg.

Kuɗaɗen da ke ƙarƙashin ikon Amurka ba su da yawa, inda aka ƙiyasta ba su wuce dala biliyan biyu ba. Kuma yawanci waɗannan kuɗaɗen na da alaƙa da hukunce-hukuncen kotu da kuma biyan diyya, abin da ya sa ba fiye maida hankali wajen sakin su ba.

Wace rawa Amurka za ta taka?

Kuɗaɗen da ke ƙarƙashin ikon Amurka ba su da yawa - ba su wuce  dala biliyan biyu ba

Asalin hoton, AFP via Getty Images

Bayanan hoto, Kuɗaɗen da ke ƙarƙashin ikon Amurka ba su da yawa - ba su wuce dala biliyan biyu ba

Duk da cewa yawancin kuɗaɗen Iran da aka riƙe ba sa cikin Amurka, amma tana da tasiri mai ƙarfi a kansu.

Waɗannan takunkumai ba Iran kaɗai suke shafa ba, har ma da bankuna, kamfanoni da gwamnatocin ƙasashen da ke hulɗa da ita.

Saboda haka, duk wata cibiyar kuɗi da ta taimaka wajen canzawa ko tura kuɗaɗen Iran, tana iya fuskantar hukunci da takunkumi ko kuma a hana ta amfani da tsarin hada-hadar kuɗi na Amurka.

A sakamakon haka, ƙasashen da ke riƙe da kuɗaɗen Iran na taka-tsantsan wajen sakin ko tura su ba tare da amincewar Amurka ba.

Wace nasara Iran za ta samu daga yarjejeniyar?

Hayaki na tashi a tsakiyar gine-gine a birnin Tehran

Asalin hoton, Anadolu via Getty Images

Bayanan hoto, Hayaki na tashi a tsakiyar gine-gine a birnin Tehran

Yarjejeniyar da Iran da Amurka suka sanya wa hannu ta tanadi hanyoyi biyu da za su iya sauƙaƙa wa tattalin arzikin Iran.

  • Yarjejeniyar za ta ba da damar sassauta wasu takunkumai domin Iran ta ci gaba da fitar da ɗanyen mai da sauran albarkatun man fetur, tare da sauƙaƙa ayyukan jigilar kaya, inshora da amfani da bankuna a kasuwancinta
  • Za ta bai wa Iran damar samun wasu daga cikin kuɗaɗenta da aka riƙe da su a ƙasashen waje, lamarin da zai ba babban bankin ƙasar iko kan yadda za a sarrafa waɗannan kuɗaɗe.

Haka kuma, yarjejeniyar za ta farfaɗo da tattalin arzikin Iran da ake hasashen darajarsa za ta kai aƙalla dala biliyan 300, wanda za a aiwatar tare da haɗin gwiwar ƙasashen yankin wanda za a cimma matsaya ta ƙarshe bayan yarjejeniyar.

Sai dai Amurka ta jaddada cewa ba za ta bai wa Iran kuɗi kai tsaye ba (abin da gwamnatin Trump ta ce ya bambanta da yarjejeniyar nukiliya ta shekarar 2015 da gwamnatin tsohon shugaban ƙasar, Barack Obama, ta cimma da Iran).

Maimakon haka, ta ce za ta mayar da hankali ne kan zuba jari a fannonin samar da ababen more rayuwa, makamashi, sufuri da sauran sassa na tattalin arziki.

Ta wace hanya kuɗaɗen za su kai ga Iran?

A zahirin gaskiya akwai ƙalubale a gaban Iran kafin ta iya samun damar amfani da kuɗaɗen, in ji Esfandyar Batmanghelidj, wanda ya kafa cibiyar bincike ta Bourse & Bazaar Foundation da ke Birtaniya.

Ya ce irin waɗannan yarjejeniyoyi na iya fuskantar ƙalubale kuma suna da "rikitarwa sosai", saboda an ce Iran za ta iya amfani da kuɗaɗen ne a cikin wata ƙasa ɗaya kawai, kuma ba ta da damar tura su zuwa wasu ƙasashe.

Shi ma Frédéric Schneider ya bayyana cewa akwai shakku sosai kan ɗorewar wata yarjejeniya.

Ya ce wasu takunkuman Amurka Majalisar Dokoki ta ƙasar ce ta kafa kuma suna cikin doka, don haka shugaban ƙasa ba zai iya cire su gaba ɗaya ba, sai dai ya sassauta su na wucin gadi.

Wannan, a ganinsa, yana haifar da rashin tabbas kan tsawon lokacin da irin wannan sassaucin zai ɗore.

Irin wannan ya taɓa faruwa bayan yarjejeniyar nukiliyar Iran ta 2015, lokacin da Iran ta samu damar amfani da wasu kuɗaɗenta. Duk da haka, bankuna da dama sun ci gaba da nuna shakku, sannan a 2018 Amurka ta fice daga yarjejeniyar tare da sake dawo da takunkumi.

A makon da ya gabata, kafafen yaɗa labaran Iran sun ruwaito cewa Amurka ta amince da sakin dala biliyan 12 na kadarorin da aka riƙe, amma har yanzu Washington ba ta tabbatar da hakan ba.

Haka kuma, akwai saɓani kan ko Amurka za ta yi amfani da wani ɓangare na kuɗaɗen wajen biyan diyya ga ƙasashen Tekun Fasha kan asarar da suka ce sun tafka a rikici.

Sakataren Baitulmalin Amurka Scott Bessent ya wallafa a shafinsa na X a farkon watan Yuni cewa "sai an biya duk wata asara da aka yi yayin rikicin daga kuɗaɗen da aka cire daga asusun Iran".

Sai dai Iran ta mayar da martani ta bakin Mataimakin Ministan Harkokin Waje, Kazem Gharibabadi, inda ta yi watsi da buƙatar, yana mai cewa kadarorin Iran "ba ganimar yaki ba ce ga Amurka, kuma ba wani asusu ba ne da za a biya abokan hulɗarta da shi".

Mene ne tasirin hakan ga tattalin arzikin Iran?

Tattalin arzikin Iran a shekarar 2024 ya kai kimanin dala biliyan 475, in ji Bankin Duniya.

Sai dai hukumomin Iran na hasashen cewa asarar da ta tafka sakamakon yaƙe-yaƙe zai iya kaiwa dala biliyan 300, yayin da tattalin arzikinta ya ragu da kusan kashi 10 a wannan shekara.

Idan aka saki ko da wani ɓangare ne na kuɗaɗen da aka riƙe, hakan zai taimaka wa ƙasar.

Wani Mamba a cibiyar kasuwanci ta Iran ya shaida wa BBC cewa ƙarancin kuɗaɗen waje ya kai wani matsayi da ya sa "harkokin kasuwanci sun tsaya cak kuma ana samun jinkiri, bayan taƙaita shigo da kayan buƙatu na yau da kullum kamar abinci".

Masana tattalin arziki sun ce samun biliyoyin daloli daga waje zai taimaka wajen daidaita darajar kuɗin ƙasar, tallafa wa shigo da kaya—musamman muhimman abubuwa—da kuma rage matsin lamba a hada-hadar kuɗi.

Sai dai sun yi gargaɗin cewa hakan ba zai warware manyan matsalolin tattalin arzikin ƙasar ba.

Kamran Nedri, farfesa a Jami'ar Imam Sadiq da ke Tehran, ya ce "ya kamata a mayar da hankali kan shawo hauhawar farashi da tsadar rayuwa kafin duk wani shirin sake gina tattalin arziki," inda ya yi gargaɗin cewa zuba kuɗi ba tare da an yi gyara ba na iya rage tasirinsu.

Sai dai wasu masana kamar Mehrdad Vahabi na Jami'ar Paris 13 sun ce babbar matsalar Iran ita ce "rashin saka jari da ta daɗe ana fama da ita".

Shi ma Reza Talebi, mai bincike a Jami'ar Leipzig, ya ce rashin tabbas tsakanin yaƙi da zaman lafiya na hana masu zuba jari shiga kasuwar ƙasar, inda ya bayyana hakan a matsayin "babbar matsala ga ci gaban tattalin arzikinta."