Ku San Malamanku tare da Munir Adamu Koza

Bayanan bidiyo, Danna hoton sama ku kalli bidiyo:
Ku San Malamanku tare da Munir Adamu Koza
An wallafa

Shirin Ku San Malamanku na wannan makon ya kari bakuncin Munir Adamu Koza, wanda haifaffen garin Mai Aduwa ne na Jihar Katsina da ke arewacin Najeriya.

An haifi malamin a ranar 1 ga watan Agustan 1986 a garin Koza.

Matashin ya fara karatun Ƙur'ani da sauran litattafan farko-farko a gaban mahaifinsa Sheikh Adam Ahmad. Ya karanta fiƙihu da tarihi a wajensa.

Ya zuwa lokacin haɗa wanna rahoton, malam yana da mata biyu da kuma 'ya'ya biyar.