Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Yan bindiga sun sace dukkan iyalan wani dan majalisar dokoki a Najeriya
'Yan bindiga sun sace ilahirin iyalan wani dan majalisar dokokin jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya.
An sace iyalan Aminu Yusuf Ardo ne ranar Alhamis da daddare a kauyensu Jangebe.
Ganau sun ce 'yan bindigar sun dirar wa gidansa da talatainin dare inda suka sace matarsa da 'ya'yansa hudu.
Bayanai sun ce dan majalisar ba ya gida a lokacin da lamarin ya faru.
Aminu Yusuf Ardo yana wakiltar mazabar Talata-Mafara ta Kudu a majalisar dokokin jihar Zamfara.
Kazalika 'yan bindigar sun sace akalla mutum takwas - yawancinsu makwabtan dan majalisar dokokin, a cewar mazauna kauyen.
Wani mutum da mahaifinsa yana daya daga cikin wadanda aka sace ya shaida wa BBC cewa sun yi matukar kaduwa yana mai cewa mutane sun yi ta zuwa domin yi musu jaje.
Ya kara da cewa kawo yanzu 'yan bindigar ba su nemi kudin fansa ba.
Kwamishinan Watsa Labarai na Jihar Zamfara, Ibrahim Magaji Dosara,ya tabbatar da kai harin sai dai ya ce har yanzu suna tattara bayanai kan batun.
A baya dai an sace mata 'yan makarantar kwana kusan 300 a makarantarsu da ke garin na Jangebe.
Sai dai daga bisani an sake su bayan an tattauna da 'yan bindigar.
Zamfara na cikin jihohin da ke fama da matsalar satar mutane domin karbar kudin fansa.